kungiyar Gamayyar kasashen Afirka ta samar wa matasa aiki a Arewa Maso Gabas

 Hadaddiyar  Gamayyar kasashen Afirka (United African State) a karo na biyu ta sake samar wa matasa 79 da suke da takardar shaidar karatun Digiri da NCE da Difloma aiki a jihohi 6 na Arewa maso Gabashin Najeriya. Da yake mika takardun shaidar samun aikin ga matasa a sakatariyar kungiya da ke Gombe, tsohon Ministan Sufuri […]

kungiyar Gamayyar kasashen Afirka ta samar wa matasa aiki a Arewa Maso Gabas

 Hadaddiyar  Gamayyar kasashen Afirka (United African State) a karo na biyu ta sake samar wa matasa 79 da suke da takardar shaidar karatun Digiri da NCE da Difloma aiki a jihohi 6 na Arewa maso Gabashin Najeriya.

Da yake mika takardun shaidar samun aikin ga matasa a sakatariyar kungiya da ke Gombe, tsohon Ministan Sufuri na Najeriya Sanata Idris Abdullahi Umar, jinjina musu ya yi na yadda suke rage zaman banza a tsakanin al’umma musammam ma Matasa.

Tsohon Ministan wanda ya samu wakilcin mai taimaka masa na musamman Alhaji Sa’idu Sambo wanda shi ma tsohon shugaban riko ne na karamar hukumar Gombe cewa ya yi ministan yana tare da su kuma shi ma zai taimaka wajen ganin ya hada kai dasu don a fadada yawan matasan.

Sanata Abdullahi Idris Umar, ya jinjina wa kokarin Hajiya Fati Usman Kulani, na yadda ta tsaya tsayin daka don ganin ta ciyar da yankin ta gaba inda ya ce da za a samu jajirtacciyar mace kamar biyar a wannan shiya da take tsayawa wajen ganin ci gaban al’umma da an magance zaman banza a tsakanin al’umma.

Daga nan sai ya ce maigidan sa ya ce ya sanar da su cewa nan gaba idan za a sake sayen takardar neman  neman guraben aikin ya dauke wa duk wani dan Gombe sannan kuma zai tsaya don ganin duk wanda ya cika fom din ya samu aikin.

Da take jawabi, shugabar wanann kungiya ta Arewa maso Gabas Hajiya Fati Usman Kulani Jakadiyar Pantami, cewa ta yi ba don kanta take wannan fafutuka ba sai don ganin ta ciyar da yankin ta na Arewa maso Gabas gaba wanda tuni sauran yankin ya yi masa fintinkau.

 Hajiya Fati Kulani, ta kara da cewa ganin an bar yanki Arewa maso Gabas a baya, anso  a can sama a mayar da cike fom din ta hanyar yanar gizo sai suka ce ba za ayi haka ba saboda wasu daga kauyuka suke basu san harkar kwamfuta sosai ba.

Sannan ta yi kira ga wadanda suka samu wannan aikin da su zama jakadu nagari a duk inda suka samu kansu dan kare martabar yankin su da kuma Arewa maso Gabas daga shiga kunya.

Haka ita ma shugabar shirin ta Jihar Bauchi Aishatu Rabi’u Sale, bayyana jin dadinta ta yi na yadda yaransu da suka gama karatu ba aikin yi yanzu suke samun madafa da suma nan gaba za ayi alfahari da su.

Haka shi ma shugaban shirin na Jihar Adamawa wanda ya rako mutanensa guda 9 da suka samu wannan aiki Abdul Sa’idu, ya jinjina wa kungiyar ne na yadda suka bullo da wannna shiri don taimakon al’umma.

Wasu da suka ci gajiyar shirin da na zanta dasu sun bayyana jin dadin sun na yadda suka jima suna neman aiki basu samu ba kasancewar a wani lokacin ana nuna musu su ba ‘ya’yan kowa bane amma yanzu suka samu aikin yi.