kungiyar Gems 4 tana inganta sana’o’i a Najeriya –Shariff
kungiyar nan mai zaman kanta ta GEMS 4 ta jaddada aniyarta ta taimaka wa kungiyoyin al’umma tare da masu kananan sana’o’i game da hanyoyin da za su inganta sana’o’insu a fadin kasar nan. Shugaba mai kula da ayyukan kungiyar Muhammad Shariff shi ne ya bayyana haka a lokacin bikin kammala wasu manyan ayyukan kungiyar a […]
kungiyar nan mai zaman kanta ta GEMS 4 ta jaddada aniyarta ta taimaka wa kungiyoyin al’umma tare da masu kananan sana’o’i game da hanyoyin da za su inganta sana’o’insu a fadin kasar nan.
Shugaba mai kula da ayyukan kungiyar Muhammad Shariff shi ne ya bayyana haka a lokacin bikin kammala wasu manyan ayyukan kungiyar a tsawon shekara biyar da suka gabata.
Da yake bayanin irin ayyukan kungiyar Muhammad Shariff ya bayyana cewa kungiyar GEMS4 ba ta bayar da kudi ga jama’a don yin jari amma tana tallafa wa masu kananan sana’oi da manoma da shawarwari kan hanyoyin da za su bi wajen inganta kasuwancinsu “Gems4 ba ta tallafa wa jama’a da jari amma tana bayar da shawarwari yadda za a inganta kasuwanci da sana’o’i, wanann shi ne abin da muka fi sanya wa a gaba.
“Mun fahimci cewa ba wai rashin sana’a ne yake damun mutane ba, illa rashin sani yadda za a bunkasa sana’a ta yadda za a rika samun gwaggwabar riba. Idan mai sana’a ba ya tunanin yadda zai inganta sana’arsa to kullum zai zauna ba tare da ci gaba ba,” inji shi.
A cewarsa a yanzu haka GEMS4 tana alfahari da samun nasarar da ta yi wajen karfafa gwiwa tare da inganta kasuwancin masu kananan sana’o’I da suka hada da ciyar da harkar noman shinkafa gaba da samar da kyakkyawar hanyar kula da tumatir don hana shi lalacewa da kuma bunkasa harkar ajiyar fata, “A da manoman tumatir suna samun asara sakamkon rashin sanin yadda za su kula da umatir din, hakan ya sa GEMS4 ta ba su horo kan yadda za su bi ta hanyar samar musu da kwandunan roba don zuba tumatir a ciki da kuma sama musu hanyar jigilar tumatir yadda ba zai lalace a hanya ba, da kuma hada manoman da kamfaninnikan da ke sarrafa tumatir.
Haka kuma GEMS4 ta hada manoman shinkafa da kamfaninnikan da ke samar musu da taki da kuma na casar shinkafa wanda hakan ya sa noman shinkafar gida ya bunkasa a jihohi 18 da ke fadin kasar nan.”
Shugaban ya kara da cewa “Har ila yau GEMS4 ta kai dauki ga harkar fata, inda ta samar wa masu harkar fata gishirin da ake amfani da shi don ajiyar fata inda za ta dauki tsawon mako uku ba tare da ta lalace ba a maimakon gishirin abinci da a da suke amfani da shi, wanda hakan ya kara daga darajar fatar .
“Haka kuma GEMS4 ta inganta harkar sarrafa shara a kasar nan inda ta sama musu hanyoyin sarrafa shara na zamani tare da samarwa dimbin al’ummar kasar nan ayyukan yi tun daga kan abin da ya shafi daukar sharar daga gidaje har zuwa mika ta ga kamaninnikan da ke sarrafa ta”
Har ila yau Muhammad Shariff ya kara da cewa baya ga sha’anin inganta sana’ao’I, GEMS4 ta shiga harkar samar da kasuwa ga masu sana’o’i musamman wadanda ke zaune a kauyuka “mun duba mun ga cewa yawancin mutanen da ke sana’o’i ko noma a kauyuka suna sayar da kayayyakinsu da arha, don rashin sana ko kuma don rashin sanin hanyar da za su kai kayan nasu kasuwannin da za a saya da daraja “GEMS4 ta kara karfafa hanyar da masu sana’ar ke sayar da kayansu inda aka kara samar musu da wasu masu karbar kayayyakin nasu a farashi mai daraja”
Wani daga cikin wadanda suka ci moriyar shirye-shiryen Gems4 da ke harkar robobi, Mustapha karaye ya bayyana cewa GEMS 4 ta taimaka masa wajen habaka kasuwancinsa “GEMS4 ta taimaka mana har mun kara bunkasa abubuwan da suke samarwa a harkar robobi da kuma yadda ma muke samun robobin wadanda muke samunsu akan hanyoyi tare da sake sarrafasu wanda hakan ya kara taimakawa wajen samar da aikin yi ga al’umma, domin mun debi ma’aikata da dama don gudanar da wadannan ayyuka.”