Kungiyar Gizago: Yadda taron shiyya ya gudana a Nasarawa
An dauki lokaci, tun bayan zaben shugabanni ana ta kai-komo wajen sake fasali da tsarin tafiyar da kungiyar Gizago ta Najeriya, a karkashin shugabancin Malam Muhammad Kabir Adam Gombe, wanda aka sani da lakanin ‘Agogo Sarkin Aiki. A kan haka ne aka kafa Kwamitin Sulhu, wanda ya rika bibiyar matsalolin da yanayin rayuwa ya samar […]
An dauki lokaci, tun bayan zaben shugabanni ana ta kai-komo wajen sake fasali da tsarin tafiyar da kungiyar Gizago ta Najeriya, a karkashin shugabancin Malam Muhammad Kabir Adam Gombe, wanda aka sani da lakanin ‘Agogo Sarkin Aiki.
A kan haka ne aka kafa Kwamitin Sulhu, wanda ya rika bibiyar matsalolin da yanayin rayuwa ya samar a kungiyar, da niyyar magance su da dinke baraka domin saita kungiyar zuwa turba tagari, bisa kyawawan manufofin da aka kirkiri kungiyar dominsu, wadanda suka hada da hadin kai, zumunci, taimakon juna da bunkasa martabar al’adun Hausa.
A ranar Asabar (06-01-2018), kwamitin ya ziyarci garin lafiya, Jihar Nasarawa, don haka, ga rahoton abin da ya wakana, kamar yadda Sakataren kungiyar Gizago ta Najeriya, Abdurrahman Abumaryam (GZG 069 KDN) ya gabatar:
Taron Kwamitin Sulhu da maido da martabar kungiya kashi na biyu, wanda ya gudana a Jihar Nasarawa.
Rahoton Taron Kwamitin: Allah Madaukaki Sarki, cikin ikonSa da kaddarawarSa, Ya kaddare mu da gudanar da taron a ranar Asabar, 6/01/2018 a garin Lafiya da ke Jihar Nasarawa domin gabatarda Taron sulhu da maido da martaban kungiyan Gizago.
Taron ya gudana kamar haka: Bude taro da addu’a, gabatarda kai, jawabin maraba daga bakin Alhaji Abdullahi Zakari, Zanwan Lafia, Uban kungiya na Jihar Nasarawa. Jawabin dalilin taron daga bakin Shugaban kungiya na kasa, Malam Muhammad Kabir Adam Gombe. Nasiha da muhinmancin sulhu daga bakin Malam Kabir Ghali Ibrahim, Ma’ajin kungiya na kasa. Gabatar da shawarwari sai kuma rufe taro da addu’a.
An bude taron da misalin karfe 10:45 na rana, sai kuma mahalarta taron suka gabatar da kai, ida kuma sai jawabin maraba da baki daga Zanwan Lafiya Alhaji Zakari Abdullahi ya biyo baya.
Tunatarwa ta biyo bayansa, wadda aka gabatar a kan muhinmancin sulhu da karfafa zumunci da sabunta shi. Malamin ya kawo ayoyi da hadisai dangane da sulhu tare da yaukaka zumunci da kuma ladan da ke tattare a cikinsa.
Daga nan sai Shugaban kungiya Gizago ta Najeriya ya kawo makasudin taron da irin nasarorin da taron ya fara samu a Jihar Kaduna, jihar da kwamitin ya fara gudanar da taronsa na farko.
A cikin jawabin nasa, ya jawo hankalin Gizagawa da su kasance tsintsinya madaurinki daya. Ya kuma yaba wa Gizagawa da irin yadda suke ba shi hadin kai a kowane lokaci. Haka kuma ya kara da cewar za su ci gaba da irin wadannan taruka domin samun ci gaban kungiya.
A karshe ya mika godiyarsa ga Gizagawan Jihar Nasarawa da kuma wadanda suka samu halartar taron. Ya kuma ce an samu jihohin da suka ba da uzuri, na rashin halartarsu, wadanda ya ce a taro na gaba za a kira su.
Bayan jawabin taron sai sai aka fara da sauraron al’amuran Gizagawan Jihar Nasarawa daga bakin shugabansu, Malam Shawailu. Ya kawo matsalolin da jihar ke fuskanta, inda ya bayyana cewa ba su da wasu matsaloli da suka wuce rashin membobi da kuma rashin zuwansu taro da rashin ba da tallafi game da bukace-bukacen kungiya.
An ba shi shawarwari game da yadda za a samu ci gaban kungiyar ta hanyoyi da dama. Daga karshe shugaba na kasa ya mika kungiya ga mai girma Zanwan Lafiya, domin samun mafita game da wadannan matsaloli.
Jihar Kogi ita ma matsalarta makamanciyar ta Jihar Nasarawa ce. Su ma an ba su shawarwari makamantan na Jihar Nasarawa kuma mai girma shugaban kungiya na kasa ya ce zai rika bibiyarsu domin jin ko suna aiki da shawarwarin da aka ba su.
Jihar Filato, su ma sun kawo korafe-korafe makamanta irin na jihohin da suka gabata, inda shugaba ya mika alhakin kungiyar ga iyayen kungiya na jihar, domin samun shawarwari.
Shugaban Gizagawan Jihar Kano ya gabatar da wata gagarumar shawara game da matakin da ya gabatar a jiharsa, ta hanyar neman tsofaffin shuwagabannin da suka gabata. An kuma jinjina masa da wannan namijin kokari da ya yi.