kungiyar Global Rights ta gudanar da taro kan ’yancin dan Adam

kungiyar kare ’yancin dan Adam ta Global Rights ta gudanar da taron karawa juna sani na kwanaki uku don fadakar da jama’a game da hakkin ’yan kasa a lokacin yaki.kungiyar ta gudanar da taron ne a Abuja a karshen makon da ya gabata, inda ta gayyaci kwararru da masana suka gabatar da kasidu a wurin […]

kungiyar Global Rights ta gudanar da taro kan ’yancin dan Adam
kungiyar Global Rights ta gudanar da taro kan ’yancin dan Adam

kungiyar kare ’yancin dan Adam ta Global Rights ta gudanar da taron karawa juna sani na kwanaki uku don fadakar da jama’a game da hakkin ’yan kasa a lokacin yaki.
kungiyar ta gudanar da taron ne a Abuja a karshen makon da ya gabata, inda ta gayyaci kwararru da masana suka gabatar da kasidu a wurin taron.
Da take jawabin maraba, Daraktar kungiyar reshen Najeriya, Abiodun Baiyewu-Teru ta bayyana cewa kungiyar ta shirya taron ne don fadakar da mutane muhimmancin ’yancin dan Adam a lokacin yaki.
Ta ce ya kamata mutane su gane cewa dan Adam yana da ’yancinsa da doka ta ba shi ko da a lokacin yaki.
Ta bayyana cewa ’yancinsa abu ne mai muhimmanci da ya zama wajibi a kiyaye a kowane yanayi.
To amma ta nuna damuwa kan yadda ake take ’yancin dan Adam ba tare da daukan matakan da suka dace ba na bin kadin wadanda aka takewa ’yanci.
Da yake jawabi, Shugaban Hukumar ba da Agajin Gaggawa ta kasa NEMA, Alhaji Muhammad Sani Sidi ya yaba wa kungiyar kan irin namijin kokarin da take yi wajen kare ’yancin dan Adam a kasar nan.
Sani Sidi wanda Alhaji Alasan Nuhu ya wakilta ya bayyana cewa an shirya taron daidai lokacin da ake bukatarsa.
“Wannan taron an shirya shi a lokacin da ya kamata musamman ma a irin wannan lokaci da ake yaki da kungiyar Boko Haram a yankin Arewa-maso-Gabas da kuma irin illar da yaki ya janyo,” inji shi.
Ya ce kamar yadda kowa ya sani yakin Boko Haram ya sanya mutane da yawa cikin wahala da asarar rayuka da dukiyoyi tare da raba jama’a da gidajensu.
Saboda haka sai ya ja hankalin mahalarta taron su yi amfani da damar da suka samu wajen wayar da kan jama’a kan illar take ’yancin bil’adama.