kungiyar GR ta nemi a kafa cibiyoyin kula da matan da aka yi wa fyade

kungiyar da ke Kare Hakkin Mata wacce ake kira da Global Rights ta yi kira ga gwamnatin tarayya da ta jihohi da su kafa sababbin cibiyoyin kula da wadanda aka yi wa fyade a yankunansu. Hakan na kunshe ne a takardar sanarwar da Shugabar kungiyar Abiodun Baiyewa-Teru ta sanya wa hannu jim kadan bayan taron […]

kungiyar GR ta nemi a kafa cibiyoyin kula da matan da aka yi wa fyade
kungiyar GR ta nemi a kafa cibiyoyin kula da matan da aka yi wa fyade

kungiyar da ke Kare Hakkin Mata wacce ake kira da Global Rights ta yi kira ga gwamnatin tarayya da ta jihohi da su kafa sababbin cibiyoyin kula da wadanda aka yi wa fyade a yankunansu. Hakan na kunshe ne a takardar sanarwar da Shugabar kungiyar Abiodun Baiyewa-Teru ta sanya wa hannu jim kadan bayan taron karawa juna sani da kungiyar ta shirya kan fyade da hanyoyin da za a yi maganinsa, a Abuja.
Shugabar ta bayyana cewa kafa cibiyoyin ya zama wajibi  saboda samun karuwar aikata fyade da cin zarafin mata da ake yi a kasar nan.
Ta ce, Najeriya tana bukatar tantance alkaluman wadanda suka aikata fyade da cin zarafin mata da yara kanana. kungiyar ta gano cewa an yi wa mata da kananan yara fyade masu yawa sannan kuma an ci zarafinsu a wurare da dama.
Kuma a ganinta akwai dokoki da aka tanada, sai dai kuma an kasa cimma burin da aka sanya a gaba na yadda dokokin za su yi tasiri ga wadanda aka samu da laifi.
Saboda haka sai ta ce ta hanyar cibiyoyin za a iya cimma burin rage fyade tare da tallafawa wadanda suka gamu da bala’in fyade. Ta ce kalubalen da ke addabar matan da aka ci zarafin su yana da mutukar muhimmaci wajen raguwar aikata fyaden.
Daga nan ta bayyana cewa mata da kananan yaran da aka ci zarafinsu na bukatar a ba su shawarar yadda za su samu kwarin gwiwar mantawa da bala’in da ya same su.
A karshe ta ce wajibi ne masu ruwa da tsaki su hada hannu wajen samar da kafar da za a cimma burin da aka sanya a gaba na kawar da halayyar fyade da cin zarafin mata da kananan yara. Don haka ta ce dole sai gwamnati da masu ruwa da tsaki sun kara kaimi wajen wayar da kan jama’a kan illar fyade da cin zarafin kananan yara.