kungiyar GR ta yi taro kan yadda za a magance fyade
Wata kungiya da ke Kare Hakkin dan Adam da Tabbatar da Adalci mai suna Global Right ta shirya taron karawa juna sani kan hanyoyin da za a bi wajen maganin matsalar fyade da kuma laifukan da suke da dangantaka da ita.Babbar Darakta kasa-da-kasa ta kungiyar, Abiodun Baiyewu-Teru, ta bayyana wa mahalarta taron a Abuja cewa […]
Wata kungiya da ke Kare Hakkin dan Adam da Tabbatar da Adalci mai suna Global Right ta shirya taron karawa juna sani kan hanyoyin da za a bi wajen maganin matsalar fyade da kuma laifukan da suke da dangantaka da ita.
Babbar Darakta kasa-da-kasa ta kungiyar, Abiodun Baiyewu-Teru, ta bayyana wa mahalarta taron a Abuja cewa kungiyar ta shirya taron ne don fadakar da jama’a illar fyade.
Ta ce yana daga cikin ayyukan kungiyar fadakar da sauran kungiyoyi tare da kara musu kwarin gwiwa kan yadda za su tunkari kalubalen fyade a cikin al’umma.
Ta bayyana cewa burin kungiyar shi ne a samu al’umma wacce ta ginu a kan kare hakkin dan Adam tare da samun adalci kamar yadda ya dace.
Ta ci gaba da cewa an kafa kungiyar ne a shekarar 1978 kuma ta yi suna wajen hada gwiwa da sauran kungiyoyi da ke yankunan karkara don cimma burin kare ’yancin bil’adama.
Da yake jawabi a wurin taron, Sufeto-Janar na rundunar ’yan sandan Najeriya, IGP Solomon Arase, ya yi kiran da a kawar da al’adun da ke karfafa yin fyade.
Arase wanda mataimakiyar Sufeto Janar ta wakilta, mai suna Chintua Amajor- Onu, ya bayyana cewa fyade wani mugun al’amari ne da ke cin zarafin bil’adama.
Ya ce ya zama wajibi ga dukkanin masu ruwa da tsaki su tashi tsaye su tunkare ta yadda ba zai yi tasiri ba a tsakanin al’umma.
Ya shawarci kungiyoyi da gwamnatoci su kafa ginshiki mai karfi da zai dakile fyade da masu yin sa don ya zama darasi ga masu sha’awar aikata shi.
A nata jawabin, Shugabar Shirin Zaman Lafiya da Sasantawa ta Jihar Barno, Hajiya Hamsatu Allamin, ta ce mata da yawa sun shiga halin ni-’ya-su saboda fyaden da aka yi musu sakamakon rikicin Boko Haram.
Ta bayyana cewa ’yan ta’adda na yin amfani da fyade a matsayin makami ga matan da suka kama tare da tursasa musu daukar juna biyu.
Ta ce matan da suka tsinci kansu a cikin wannan hali suna fama da tsangwama da nuna musu wariya da jama’a suke yi.
Daga nan ta shawarci al’umma da gwamnatoci su tashi tsaye wajen maganin tsangwamar da ake yi wa matan da suka gamu da ibtila’in fyade.