kungiyar Hada kan Matasa ta yi aikin gyaran hanya a Jos
Wasu matasan da ke zaune a Unguwar Rimi ta garin Jos, babban birnin jihar Filato, sun gudanar da aikin gyaran hanyar unguwar a karshen makon da ya gabata.Matasan sun gudanar da wannan aiki ne ta hanyar aikin gayya. Da yake zantawa da wakilinmu a lokacin da suke gudanar da wannan aikin gayya, shugaban kungiyar hada […]
Wasu matasan da ke zaune a Unguwar Rimi ta garin Jos, babban birnin jihar Filato, sun gudanar da aikin gyaran hanyar unguwar a karshen makon da ya gabata.
Matasan sun gudanar da wannan aiki ne ta hanyar aikin gayya. Da yake zantawa da wakilinmu a lokacin da suke gudanar da wannan aikin gayya, shugaban kungiyar hada kan matasan unguwar, Salmanu Hassan Dikko ya bayyana cewa a duk lokacin da damina tazo sukan hadu su gudanar da wannan aiki na gyaran wannan hanya. Domin idan damina tazo ruwa yana zaizaye hanyar unguwar.
Ya ce: “A wannan aiki mun cike wuraren da suka zaizaye da duwatsu da kasa da kuma kankare. Kuma babban abin da ya karfafa mana gwiwar yin wannan aiki, shi ne domin mu ba da gudunmawarmu wajen taimakawa al’ummarmu samun saukin bin wannan hanya a lokacin damina’’.
Salmanu Hassan Dikko ya yi bayanin cewa a wannan aiki sun sami taimakon kasa da karyayun bulo daga masu gidajen bulo da ke wannan unguwa. Kuma sun sami tallafi daga sauran jama’ar unguwar.
Ya ce “baya ga wannan aiki yanzu kuma za mu ci gaba da aikin gyaran magudanun ruwa da ke wannan unguwa. Don haka muna bukatar matasan wannan unguwa da sauran al’ummar wannan unguwa su ba mu goyan baya da hadin kai kan wadannan ayyuka da muka sanya a gaba,” inji shi.