Kungiyar Hausa Fasaha ta Karrama ’Yar Jarida a Gombe
Kungiyar Hausa Fasaha ta Makarantar Sakandare Al’umma ta Shehu Abubakar da ke Gombe (Shehu Abubakar Community Secondary School) ta karrama wata fitacciyar ’yar Jarida Malama Salamatu Wanbai Aliyu Zambuk, da wasu Hakimai da lambar yabo. Kungiyar ta karrama mutanen ne a lokacin bikin yaye dalibanta na shekara ta 2017 a harabar Makarantar inda kafin bada […]

Kungiyar Hausa Fasaha ta Makarantar Sakandare Al’umma ta Shehu Abubakar da ke Gombe (Shehu Abubakar Community Secondary School) ta karrama wata fitacciyar ’yar Jarida Malama Salamatu Wanbai Aliyu Zambuk, da wasu Hakimai da lambar yabo.
Kungiyar ta karrama mutanen ne a lokacin bikin yaye dalibanta na shekara ta 2017 a harabar Makarantar inda kafin bada wannan lambar yabo aka gudanar da jawabai daban daban na ganin an ciyar da harshen Hausa gaba a duniya baki daya.
Da take jawabi a wajen taron Kwamishinar Ma’aiktar Ilimi ta jihar Hajiya Aishatu Muhammed Bose Ahmed ta jinjina wa wannan kungiya da cewa abubuwan da suke gudanarwa abu ne da zai kawo ci gaban al’umma.
Kwamishinar wacce ta yi magana ta bakin Babban Sakataren Ma’aikatar Alhaji Abdulkadir Usman wanda shi ma yana cikin wadanda aka karrama din ta ce bai san me zai fadaba kan wannan lamba da aka ba shi domin abun farin ciki ne da kuma alfahari a ce wata kungiya ta harkar ilimi ta karrama ka a tafarkin aikin ka.
Alhaji Abdulkadir Usman, ya kuma yaba wa Malama Salamatu Wanbai Aliyu Zambuk, na yadda ta gabatar da makala a kan muhimmancin ilimin ’ya’ya mata inda yace bai wa mata fifiko wajen samun ilimi shi ke kara bai wa yara tarbiya a gida.
Babban Sakataren, ya yi kira ga dalibai da cewa saboda muhimmanci da ilimin ’ya mace yake da shi, yanzu haka a gwamnati jihar ta gina karin wasu makarantun kwana na mata kuma karatun kyauta ne daga aji daya na karamar Sakandare har zuwa aji shida.
A na ta jawabin, Malama Salamatu Wanbai, wacce tsohuwar ma’aikaciya ce a gidan Rediyon Jihar Gombe da kuma Progress FM da yanzu haka take taimakawa da shirye shirye a gidan Radiyon Ray Power FM, jawo hankalin iyaye ta yi wajen bai wa ’ya’ya mata fifiko a wajen karatu domin tarbiyar ’ya mace kamar tarbiyar al’umma ce.
Malama Salamatu Wanbai Aliyu, ta yi kira ga ‘ya’yan wannan kungiya ta Hausa Fasaha da kar su tsaya a iya wasan kwaikwaiyo da suke yi, su nemi wata hanya da za su hada kai da wata kafar yada labarai suna kara nuna wa jama’a muhimmancin wannan harshe na Hausa.
Daga nan sai ta gode wa Allah da shugabani da membobin kungiyar na yadda suka zakulo ta a cikin sauran ba dan tafi kowa ba aka karrama ta da wannan lambar yabo.
Wadanda aka karrama sun hada da Babban Sakataren Ma’aikatar Ilimin da Salamatu Wanbai da Hakimin Pantami da kuma Hakimin Bolari Alhaji Abubakar Garba Abubakar.