kungiyar Hausawan Ekiti ta bukaci ’ya’yanta su rika bin doka da oda
kungiyar Matasan Hausawan Jihar Ekiti sun bukaci ’ya’yanta sun rika bin doka da oda, su kuma kasance masu son zaman lafiya.Shugaban kungiyar Kwamared Nuhu Lawal ne ya bukaci hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata, inda ya raraba ta ga .Shugaban ya ce Hausawa na zaune lafiya a Ekiti sama da shekara […]
kungiyar Matasan Hausawan Jihar Ekiti sun bukaci ’ya’yanta sun rika bin doka da oda, su kuma kasance masu son zaman lafiya.
Shugaban kungiyar Kwamared Nuhu Lawal ne ya bukaci hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata, inda ya raraba ta ga .
Shugaban ya ce Hausawa na zaune lafiya a Ekiti sama da shekara 30, inda suke gudanar da kasuwanci domin habaka tattalin arzikin wannan yankin da kasa baki daya, don haka ya bukaci su ci gaba da zama lafiya hade da bin doka da oda.
Ya ce sun kafa kungiyarsu ne don hada kan Hausawa da ke Jihar Ekiti, sannan su dinke duk wata baraka da ke iya tasowa tsakaninsu da mutanen Kudu.
Shugaban ya nuna matukar damuwarsa dangane da mawuyacin halin da Arewa ta shiga sakamakon matsalar rashin tsaro.
“Ya zama dole a tashi tsaye wajen yin addu’o’i, sannan a rika taimaka wa jami’an tsaro da muhimman bayanai don kawo karshen matsalar tsaro.
Ya ce sun kafa kungiyarsu a shekarar 2012 domin yin magana da murya daya a madadin matasan Hausawan da ke zaune a kananan hukumomi 16 a Jihar Ekiti, inda ta zamo hanyar kare mutuncin Hausawan da ke zaune a jihar.
A karshe, ya bukaci ’yan kungiyar su kasance masu hakuri, su rika hada kansu, don a samu ci gaba da kuma zaman lafiya.