kungiyar HiLWA ta nemi a kara wa mata kaso a fannonin ilmi a Jihar Katsina

kungiyar mata ta ‘’HiLWA (High Lebel Women Adbocacy) ta Jihar Katsina ta yi kira da a samar da dokar da za ta kara wa mata wani kaso a cikin harkokin ilmi tare da sauran mukamai zuwa kashi talatin da biyar cikin dari (35%) sabanin kashi tara da digo biyar(9.5%) da jihar ke ba su a […]

kungiyar HiLWA ta nemi a kara wa mata kaso a fannonin ilmi a Jihar Katsina

kungiyar mata ta ‘’HiLWA (High Lebel Women Adbocacy) ta Jihar Katsina ta yi kira da a samar da dokar da za ta kara wa mata wani kaso a cikin harkokin ilmi tare da sauran mukamai zuwa kashi talatin da biyar cikin dari (35%) sabanin kashi tara da digo biyar(9.5%) da jihar ke ba su a halin yanzu. 

Taron da kungiyar ta kira na masu ruwa da tsaki ya gudana ne a dakin taro na Makera Motel da ke cikin garin Katsina domin samun shawarwarin yadda za a samar da daftarin tsarin dokar wanda ake fatan amincewa da shi a jihar. 

A jawabinta, shugaban kungiyar Hajiya Mariya Abdullahi ta ce wannan taro ci gaba ne daga sauran tarurrukan da kungiyar ta yi a kan wannan manufa ta bai wa mata ilmi musamman kananan ‘yan mata wanda ta ce yana daga cikin koma bayan da ake samu a Arewacin kasar nan. Shugabar ta ce wannan matsala ta karancin ilmin yara mata da kuma samar da wasu mukamai a matakan gwamnati na daya daga cikin ababen da ka kawo matsala a wajen samun ingantaccen ilmi ga matan wanda kuma ko addini bai hana neman ilmi ba ga kowa. 

Hajiya Mariya ta kara da cewa an kaddamar da wannan shiri wanda yake hadin gwiwa ne da kungiyar da ke tallafawa kananan yara ta duniya Unicef da jihohin Bauchi da Katsina da Neja da Sakkwato da Zamfara a cikin watan Afirailun 2014 a hedkwatar ma’aikatar ilmi ta Tarayya da ke Abuja. 

Daga baya an samu karin shigowar wasu jihohin cikin wannan shiri kamar su Adamawa da Borno da Kebbi da Yobe, “Yunkurin HiLWA shi ne na ganin ta tallafa wajen ciyar da ilmin yara mata gaba tare da ganin cewa ana sanya su a makarantu tare da ganin ana daukar mata a matsayin sakatarorin ilmi da Daraktoci da sauran shugabanci a sassan hukumomin ilmi a Jihar Katsina,” inji shugabar kungiyar. 

An gabatar da kasidu da shawarwari domin ganin cewa an samar da daftarin tsarin wannan doka wadda ake fatan samun amincewar Majalisar Dokokin jihar tare da sa hannun gwamna kamar yadda Jihar Zamfara ta samar da wannan doka.

Mahalarta taron sun hada da malaman addini da kungiyoyi da sarakuna da masa shari’a tare da wasu kafofin yada labarai karkashin jagorancin shugaban taron Mai shari’a Musa danladi.