Kungiyar Ingilishi ta Dambatta ta horar da daliban da ke shirin shiga jami’a

Kungiyar Habaka Harshen Ingilishi da Adabinsa ta Dambatta ta gudanar da taron da ta saba duk shekara don horar da dalibai masu shirin rubuta jarrabawar shiga manyan makarantu (JAMB) wadanda suka fito daga yankunan Dambatta da Makoda A yayin wannan taro kungiyar ta gayyato jami’an Hukumar JAMB, Shiyyar Kano a karkashin jagorancin Malama Safiyya Harazumi, […]

Kungiyar Ingilishi ta Dambatta ta horar da daliban da ke shirin shiga jami’a

Kungiyar Habaka Harshen Ingilishi da Adabinsa ta Dambatta ta gudanar da taron da ta saba duk shekara don horar da dalibai masu shirin rubuta jarrabawar shiga manyan makarantu (JAMB) wadanda suka fito daga yankunan Dambatta da Makoda

A yayin wannan taro kungiyar ta gayyato jami’an Hukumar JAMB, Shiyyar Kano a karkashin jagorancin Malama Safiyya Harazumi, inda suka gabatar da jawabai kan rajistar jarrabawar  da matakan da ake bi wajen yi da darussan da za a zaba, ciki har da darasin Ingilishi wanda yake a matsayin wajibi.

Jami’an Hukumar JAMB din sun horar da daliban kan cibiyoyin da za su je wajen yin  jarrabawar, sun kuma gargadi mata game da yin kunshi a yatsu da sauransu.

A nasa jawabin tunda farko, Sakataren Kungiyar Malam Sa’idu Mustapha Buhari, ya ce kungiyar tana shirya wannan bita ce don fadakar da daliban da ke shirin rubuta jarrabawa da wayar musu da kai game da yadda za su rubuta jarrabawar.

A jawabin Malam Sabi’u Bala, gode wa Hukumar JAMB ya yi bisa samun damar halartar taron da suke yi duk shekara duk da tarin ayyukan da ke gabansu. Sannan ya yi kira ga daliban kan su yi aiki da abin da suka koya a wajen bitar.

Kabiru Ahmad Isa daga Kwalejin Fasaha ta Gwamnati da ke Dambatta da Umma Salama Lawan daga Makarantar Sakandaren Fatima a Dambatta sun nuna jin dadinsu tare da gamsuwa da bitar, tare da shan alwashin yin aiki da abin da suka koya.

Aminiya ta gano cewa fiye da dalibai 300 ne suka halarci wannan horarwa.