Kungiyar Injiniyoyi na Kafanchan ta gudanar da taronta
Bincike ya nuna kimanin mutum dubu 3, 242 ne su ke rasa rayukansu a sanadiyyar hadarurrukan da suka shafi kan hanya wanda hakan ya sa asarar rayukan da ake yi a sanadiyyar hadarin mota ya zamo hanya mafi girma na rasa rayuka baya ga cututtuka masu yaduwa a cikin mutane. Injiniya Ibrahim Paul Yushau na […]
Bincike ya nuna kimanin mutum dubu 3, 242 ne su ke rasa rayukansu a sanadiyyar hadarurrukan da suka shafi kan hanya wanda hakan ya sa asarar rayukan da ake yi a sanadiyyar hadarin mota ya zamo hanya mafi girma na rasa rayuka baya ga cututtuka masu yaduwa a cikin mutane.
Injiniya Ibrahim Paul Yushau na hukumar kiyaye hadarurruka (FRSC) ne ya bayyana haka a wajen taron wata-wata da kungiyar Injiniyoyi na kasa (NSE) reshen Kafanchan ke gudanarwa wanda aka kammala a tsangayar horar da dabarun noma a Kwalejin Kimiyya da kere-kere ta Nuhu Bamalli da ke Samarun Kataf da ke karamar Hukumar Zangon Kataf na Jihar Kaduna.
Yusha’u, wanda ya bayyana rashin kyawun ababen hawa da rashin ingancin hanyoyi masu kyau a matsayin wasu daga cikin dalilan da ke yawan haddasa hatsarurruka a kasar nan, ya yi kira ga masu tuki da su rika lura da alamomin da ke kan hanya domin a cewarsa, ba dukanin masu tuki ne su ka fahimci abin da alamomin ke dauke da su ba sannan, ya hori direbobi da su zamo masu bin dokokin hanya yayin tafiye-tafiyensu.
Shi kuwa da yake nasa jawabin, Injiniya Thomas Barna Lass, daga Kwalejin Ilmi ta Jihar Kaduna da ke Gidan Waya-Kafanchan ya yi bayani ne a kan yadda dan adam zai bunkasa fikirarsa a daidai zamanin da ake ta kirkiro na’urorin da su ke yin aiki irin na mutane wanda wasu ke tunanin hakan wata barazana ce da za ta haifar da marasa aikin yi sanadiyyar yin na’urorin da za su rika yin aiki a madadin mutane inda ya ce hakan zai dada shajja’a mutane ne kawai da kuma kara musu himma wajen ci gaba da kirkire-kirkire domin na’urorin ma na sarrafuwa ne da irin yadda dan adam ya gina su a bisa tunaninsa.