kungiyar Izala fitilar al’umma ce
kungiyar Izala ta kasance fitila da ta haskaka zuciyar al’ummar Najeriya, domin kuwa yanzu haka wannan kungiyar mai cike da albarka, ta taimaka sosai wajen yaki da jahilci a tsakanin maza da mataa tarayyar Najeriya da ma Yammacin Afrika.Shekaru goma kacal da suka wuce idan ka je wasu garuruwan, musamman karkara za ka tar0ar da […]
kungiyar Izala ta kasance fitila da ta haskaka zuciyar al’ummar Najeriya, domin kuwa yanzu haka wannan kungiyar mai cike da albarka, ta taimaka sosai wajen yaki da jahilci a tsakanin maza da mata
a tarayyar Najeriya da ma Yammacin Afrika.
Shekaru goma kacal da suka wuce idan ka je wasu garuruwan, musamman karkara za ka tar0ar da yadda gargajiya da ayyukan zunubai su kayi tasiri a cikin zukatan al’umma, ayyukan masha’a da suka hada da shan giya,yanda a waccen lokacin ya zama ruwan dare a tsakanin manya da yara a waccen lokacin da Chacada karta da budar kai a bukukuwan auratayyar Hausa-Fulani, kai wasu garuruwan ma har sallar idi da kida suke zuwa, da dai sauransu. amma sanadiyyar shiga lungu da sako dama birni da kauye suna gabatar da wa’azi hakan ya taimaka sosai wajen rage manyan zunubai irin wadanda na lissafo a baya.
Zan kuma yi amfani da wannan daman don na yi kira zuwa ga adalin shugaba Sheikh Abdullahi Bala Lau da ma daukacin shugabannin wannan kungiya mai albarka da su kirrkiro da jami’a ta musamman da zai ta mayar da hankali kacokan akan harkokin addinin Musulunci. Saboda wannan yunkurin zai kara sa matasanmu su tashi da tarbiyya irin na addini Musulunci.
Sannan kuma kamar yadda wannan kungiya mai albarka ta yi fice wurin taimaka wa marayu karkashin jagorancin adalin shugaba sheikh Abdullahi Bala Lau,zan kuma kara kira zuwa ga wannan shugaba da ya kirkiro da wata sabuwar asusu ta musamman da zai na tallafa wa dalibai wadda iyayensu ba su da galihu, domin su ma su sami damar zuwa karatu a kakashen duniya a fannonin karatu da da ma don su dawo, su kara tallafa wa Musulunci da Musulmi a Najeriya.
Daga karshe dai kuma da fatan ‘yan kasuwar mu za su yi amfani da wannan watan mai albarka da muke gab da shigarta don su kara rage farashin kayan masarufi, don kara samun ladan da rahamar da ke kunshe a cikin watan ramadana.
Ya Allah ka kara daukaka Musulunci da Musulmi, Ya Allah ka gafarta mana zunubanmu, ko mun samu sawaba a Najeriya, ya Allah ka wanzar mana da zaman lafiya a Najeriya, Ya Allah ka ba mu damuna mai albarka.
Kwamared Abdulwahab Haladu Zarma Hina(Shugaban Jin dadi da walwala na kungiyar Muryar Talaka na kasa) 07060417970.