kungiyar Izala ta bullo da shirin horar da matasa ayyukan yi
kungiyar Jama’atu Izalatil Bidi’a Wa Ikamatis Sunnah (JIBWIS) ta kasa ta bullo da shirin koya wa matasa aikin dogaro da kai, kamar yadda shugabanta, Shaikh Abdullahi Bala Lau ya bayyana wa ’yan jarida a Yola. Ya ce ganin gazawar gwamnatoci a kasar nan kan inganta rayuwar al’umma, musamman matasa, ya sa kungiyar ta JIBWIS ta bullo […]
kungiyar Jama’atu Izalatil Bidi’a Wa Ikamatis Sunnah (JIBWIS) ta kasa ta bullo da shirin koya wa matasa aikin dogaro da kai, kamar yadda shugabanta, Shaikh Abdullahi Bala Lau ya bayyana wa ’yan jarida a Yola.
Ya ce ganin gazawar gwamnatoci a kasar nan kan inganta rayuwar al’umma, musamman matasa, ya sa kungiyar ta JIBWIS ta bullo da shirin don kyautata rayuwar matasa, maimaikon halin da ’yan siyasa suna jefa su ciki, na amfani da kudi da ikon da suke da shi wajen tursasa su shiga bangar siyasa da shan miyagun kwayoyi.
Shaikh Bala Lau ya ce ’yan siyasa, a matsayinsu na shugabanni, ya kamata a ce su ke gaba-gaba wajen shirya tsare-tsare da gabatar da ingantattun manufofi na kafa matasa da inganta rayuwarsu ta yadda za su zama abin alfahari da koyi a cikin alumma saboda gaba.