kungiyar Izala ta fadakar kan illar shirka a Legas
kungiyar Izalatul Bid’a Wa Ikamatus Sunnah, karkashin jagorancin Shaikh Bala Lau ta gudanar da taron wa’azi a Legas don fadakar da dokokin addinin Musulunci.Taron wa’azin, wanda aka gudanar a unguwannin Agege da Festac a karshen makon da ya gabata, ya samu halartar fitaccen mai wa’azin nan Malam Kabiru Haruna Gombe, wanda shi ne sakatare-janar na […]

kungiyar Izalatul Bid’a Wa Ikamatus Sunnah, karkashin jagorancin Shaikh Bala Lau ta gudanar da taron wa’azi a Legas don fadakar da dokokin addinin Musulunci.
Taron wa’azin, wanda aka gudanar a unguwannin Agege da Festac a karshen makon da ya gabata, ya samu halartar fitaccen mai wa’azin nan Malam Kabiru Haruna Gombe, wanda shi ne sakatare-janar na kungiyar, kuma yayin da yake gabatar da wa’azin, ya bukaci al’ummar musulmi su guji shirka saboda hadarinta. “Ya zama wajibi al’ummar musulmi su guji yi wa Allah kishiya, lamarin da ke janyo asara duniya da lahira. Ya zama dole su tsaya kan tauhidi, wato kadaita Allah wajen bauta da kuma tabbata kan tafarkin sunna, kada su bari mai rudi ya rude su ta kowace hanya”. Inji shi.
Ya ci gaba da cewa, “Tsayawa kan tauhidi shi ne zaman lafiyar kowane dan Adam, amma kauce wa umarnin Allah shi yake janyo rashin zaman lafiya da kwanciyar hankali, domin Allah Ya kyamaci shirka”.
Malam Kabiru Gombe ya bayyana cewa kungiyar ta bullo da tsare-tsare don inganta ayyunkanta. “Akwai katin waya da mutum zai saya ya sanya lambobin katin a wayarsa ya aikta da shi, nan take za a yi masa rajista kuma ta haka za a gane gari da jiha da kuma masallacin da mutum yake. Nan ba da jimawa ba kungiyar za ta daina yawo da kokon bara don neman taimako, sakamakon sabon tsarin da ta bullo da shi. Da zarar mutum ya sayi kati ya sa a wayarsa sai a cire iyakar gudunmawar da ya amince a cire. Ta haka za mu rika gudanar da dawainiyar wa’azuzzukanmu da ginin masallatai da asibitoci da kula da marayu da sauran ayyukan kungiya”. Inji shi
Manyan bakin daga sassa da dama na Jihar Legas da wasu wurare makwabta suka halarci taron wa’azin, wanda aka gudanar cikin kwanciyar hankali da lumana.