Kungiyar Izala ta gudanar da taron wayar da kan ’yan agaji

kungiyar Jama’atu Izalatil Bidi’ah Wa Ikamatis Sunnah reshen Jihar Nasarawa ta gudanar da wani gangamin don wayar da kan ’yan agaji a garin Doma da ke Jihar Nasarawa. Shugaban kungiyar na Jihar, wanda ya jagorranci taron Alhaji Abubakar Sa’id Alkafawee ya ce makasudin shirya wannan haduwa shi ne don bayar da horo tare da wayar […]

Kungiyar Izala ta gudanar da taron wayar da kan ’yan agaji
Kungiyar Izala ta gudanar da taron wayar da kan ’yan agaji

kungiyar Jama’atu Izalatil Bidi’ah Wa Ikamatis Sunnah reshen Jihar Nasarawa ta gudanar da wani gangamin don wayar da kan ’yan agaji a garin Doma da ke Jihar Nasarawa.

Shugaban kungiyar na Jihar, wanda ya jagorranci taron Alhaji Abubakar Sa’id Alkafawee ya ce makasudin shirya wannan haduwa shi ne don bayar da horo tare da wayar da kan ’yan agaji a jihar baki daya kan sanin makamar aiki da kuma karantar da su tsare-tsaren aikin domin su tashi da kyakkyawar manufa da tarbiyya bisa koyarwar addinin Musulunci.
Ya ci gaba da cewa “Wannan aiki ya samo asali ne tun daga lokacin Manzon Allah (SAW) da ya koya wa sahabbansa irin wannan aiki sannan marigayi Sheikh Isma’ila Idris Zakariya Jos ya kafa kungiyar da aka fi sani da Jama’atu Izalatil Bidi’ah Wa Ikamatis Sunnah ta kasa baki daya.”
A cewarsa Sheikh Zakariya ya kuma kafa reshen agajin kungiyar wanda a lokacinsa ne aka fara gabatar da wannan aiki. Ya kara da cewa wannan taron yana daga cikin wadanda ba za a taba mantawa da su ba kasancewar ya samu halartar manyan baki daga kungiyar ta kasa da kuma tsofaffin shugabannin kungiyar a jihar kamar Alhaji Isma’ila Shu’aibu Bature da Alhaji Abdullahi Maikasuwa da Shugaban Agaji na  Abuja, Alhaji Abubakar Abdulhamid da sauransu.
 Daga nan sai shugaban ya yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta tsaya tsayin daka wajen gano gaskiyar abin da ya faru a tsakanin ’yan Shi’a da sojoji a garin Zariya. Kuma ya yi kira ga kungiyoyin kare hakkin dan Adam su dauki matakan da suka dace kan lamarin. Har ila yau, ya yi kira ga ’yan Shi’a su ji tsoron Allah su daina aibanta sahabban Manzon Allah (SAW) da iyalan gidansa, inda ya bayyana hakan a matsayin “kafirci da tawaye ga addinin Musulunci.”  
A karshe ya yi ta’aziyya ga iyalan mahajjata da suka rasa rayukansu lokacin aikin Hajjin bana a kasar Saudiyya.