kungiyar Izala ta tallafa wa mabukata 2,500 a Jihar Filato
kungiyar Jama’atu Izalatil Bid’ah Wa’ikamatis Sunnah (JIBWIS), reshen Jihar Filato ta tallafa wa marayu da gajiyayyu da zawarawa sama da 2,500 da suka fito daga kananan hukumomin jihar da kayayyakin abinci da tufafi da kudi. Shugaban reshen kungiyar, Alhaji Iliyasu Umar Wushishi ne ya bayyana haka, a lokacin da yake zantawa da wakilinmu, inda ya […]
kungiyar Jama’atu Izalatil Bid’ah Wa’ikamatis Sunnah (JIBWIS), reshen Jihar Filato ta tallafa wa marayu da gajiyayyu da zawarawa sama da 2,500 da suka fito daga kananan hukumomin jihar da kayayyakin abinci da tufafi da kudi.
Shugaban reshen kungiyar, Alhaji Iliyasu Umar Wushishi ne ya bayyana haka, a lokacin da yake zantawa da wakilinmu, inda ya nuna cewa an tallafa wa marayu 1,200 da gajiyayyu 1,100 kuma zawarawa 200.
Ya ce da ma sun saba gudanar da wannan shiri a kowace shekara, amma bayan da shugaban kungiya na kasa, Sheikh Abdullahi Bala Lau ya kara karfafa masu gwiwa, sai abin ya fi na kowace shekara. “Mun umarci shugabannin reshen kowace karamar hukuma kan su tabbatar da an aiwatar da shirin a sassansu. Mun tallata bukatar tallafi a masallatanmu, tun kafin watan azumin da ya gabata, kuma al’ummar musulmi suka kawo mana wadannan kayayyaki na abinci da suturu.
“Babban burinmu kan gudanar da wannan shiri shi ne sanya natsuwa a zukatan wadannan marayu da gajiyayyu da zawarawa su rika jin kamar suna tare da iyayensu ko kuma abin da suka rasa na halin rayuwa da suke ciki”. Inji shi.
A karshe ya yi kira ga al’ummar musulmi su hada kai kuma su kara kokari wajen taimaka wa junansu.