kungiyar Izala ta tallafa wa marayu a Legas

A ranar Talatar da ta gabata ce Haɗaɗɗiyar kungiyar Jama’atul Izalatil Bidi’a Wa Iƙamatus Sunnah mai hedikwata a Jos reshen Jihar Legas ta ba marayu sama da 200 tallafi domin su ma su sami ikon gudanar da bukukuwan Sallah ƙarama cikin walwala da annushuwa.Sakataran ƙungiyar, Malam Muhammadu Auwal ya shaida wa Aminiya cewa ƙungiyar ta […]

kungiyar Izala ta tallafa wa marayu a Legas
kungiyar Izala ta tallafa wa marayu a Legas

A ranar Talatar da ta gabata ce Haɗaɗɗiyar kungiyar Jama’atul Izalatil Bidi’a Wa Iƙamatus Sunnah mai hedikwata a Jos reshen Jihar Legas ta ba marayu sama da 200 tallafi domin su ma su sami ikon gudanar da bukukuwan Sallah ƙarama cikin walwala da annushuwa.
Sakataran ƙungiyar, Malam Muhammadu Auwal ya shaida wa Aminiya cewa ƙungiyar ta tallafa wa marayun da kuɗi Naira dubu ɗari biyar da bandir ɗin atamfa 30 da na yadidduka 25. Kana ta biya wa iyayen marayun kuɗin gidan haya duba da tsadar haya da ake fama da ita a Legas. Bugu da ƙari, ta tallafa wa wasu dattawa gajiyayyu da kuɗin kulawa da lafiyarsu, abin da ya shafi magunguna da makamantansu, kana ya ƙara da cewa tallafin da haɗaɗɗiyar ƙungiyar ta bayar a Legas bai tsaya kan ’yan ƙungiyar kaɗai ba, domin hatta waɗanda ba ’yan ƙungiyar ba sun amfana da taimakon.
A cewar shugaban gidaniyar tallafin, Alhaji Hashimu Usman an haɗa waɗannan kayayyaki da kuɗi Naira dubu 500 ne a ranar 20 ga watan Ramadan, ranar da aka ƙaddamar da gidauniyar; inda mutanen Agege da sauran sassa na Jihar Legas suka ba da gagarumar gudunmawa, duba da irin kiraye-kirayen da Sheikh Murtala Abubakar Imam Jingir ya yi ta yi, tun lokacin da ya soma jagorantar karatun tafsirin Alƙurani a farkon watan azumi.
“Taimakon marayu da marasa ƙarfi aƙida ce ta Musulmi, ganin yadda muka yunƙuro muna ta samun ƙaruwar marayu da mabuƙata, don haka ƙofar neman taimakon a buɗe take ga duk mai niyya, domin shi taimakon ga marayu bai taƙaita ga watan Ramadana kawai ba.” Inji shi.
Shaikh Murtala Abubakar Imam Jingir ya yaba da yadda mutanen Legas suka baiwa shirin goyon baya, ya kuma yi addu’ar Allah Ya ruɓanya masu dukiyar da suka fitar tare da basu ladan ayyukan alherin da suka gabatar.
Haka zalika, ƙugiyar Izala reshen garin Abekuta a Jihar Ogun, mai hedikwata a Kaduna ta ba da irin wannan tallafi ga marayu da zawarawa da marasa galihu da tsofaffi maza da mata a garin Sabo Abekuta. Sakataren ƙungiyar, Alhaji Zakariyya Musa Magaji, wanda aka fi sani da Ɗanladi Sufi, ya shaida wa Aminiya cewa ƙungiyar ta ba da tallafin kuɗi Naira 56,765 da turamen atamfa, da na shadda guda 30 da kayyayakin abinci waɗanda suka haɗa da shinkafa da taliya da dai sauransu.  Ya ce an samu nasarar tattara kayayyakin ne bayan da Sheikh Yahaya Usman ya jagoranci ƙaddamar da gidauniyar tallafa wa marayu a ranar 20 ga watan Ramadan a Abekuta.