kungiyar Izala ta yaye dalibai 45 a Benin

A wannan makon ne makarantar kngiyar Izalatul Bidi’a Wa ikamatus sunna reshen Jihar Edo ta yaye dalibai 45 na Shababu Ummatul islamiyya, reshen makarantar Usmanu Bin Affana da ke unguwar Eyaen a garin Benin inda ta kuma karrama wasu daga cikin malamai masu koyarwa a makarantar, wadanda suka hada da babban limamin masallacin Juma’a na […]

kungiyar Izala ta yaye dalibai 45 a Benin
kungiyar Izala ta yaye dalibai 45 a Benin

A wannan makon ne makarantar kngiyar Izalatul Bidi’a Wa ikamatus sunna reshen Jihar Edo ta yaye dalibai 45 na Shababu Ummatul islamiyya, reshen makarantar Usmanu Bin Affana da ke unguwar Eyaen a garin Benin inda ta kuma karrama wasu daga cikin malamai masu koyarwa a makarantar, wadanda suka hada da babban limamin masallacin Juma’a na kungiyar da ke Eyaen, Ustaz Abdulrahman Abdallah da Malam Ibrahim Shagamu da Malam Abubakar .S.Dauda.
Darakta mai kula sashin koyar da Addinin Musulunci na makarantar, Ustaz Usman Saidu Elkanawi ya bayyana wa Aminya cewa, an kikiro wannan sashi na Shababu Ummatul Islamiyya a karkashin makarantar Usmanu Bin Affana ta kungiyar Izala don koyar da matasa.  
“Manufarmu ta kikiro wannan sashin, ita ce, hanyar koyarwa da wayar wa matasa kansu akan abin da ya shafi addinin Musulunci, tare da koya musu ilimin zamani da sana o’in dogaro da kai,” inji shi.
 A cewarsa, wannan ya sanya muka kasa wannan sashin kamar haka, wato akwai bangaren koyon rubutu da karatun Larabci da na Boko, akwai bangaren karatun Alkur’ana da harshen Larabci da Ingilishii da lissafi da sauran wasu fannonin ilimin addini da harkar kasuwanci na zamani.
daliban da suka kammala karatunsu, kuma muka yaye su akwai wadanda suka kware a harshen Larabci da Turanci, kuma akwai wadansu da  suka yi haddar Alkur’ani gwargwadon hali. Wadannan daliban mun bai wa kowannensu takardar shaidar kammala karatu a wannan  sashi na Shababu Ummatul Islamiyya na Makarantar Usman Bin Affana.
A wannan walimar, malamai sun yi nasihohi masu dama, tare da yin kira akan neman ilimi na kowane fanni, sun kuma yi gargadi akan miyagun mutane da ke kokarin cusa wa mutane wata akida, ta  kyamar ilimin zamani, sun ce wannan babu wata hujja ta gaskiya, illa kawai jahilci da son rai da ya samu gindin zama a zukatan wasu ’yan damfara.