kungiyar Izala ta yi wa malaman tafsiri taron bita a Gombe

kungiyar Jamaátu Izalatil bidiá wa íkamatissunnah ta kasa, reshen Jihar Gombe ta gudanar da taron bita, a cibiyar ilmi, ga malamai da limamanta kafin su fara gudanar da tafsirai na bana a jihar.A jawabinsa, shugaban kungiyar na jiha, Alhaji Salisu Muhammad Gombe, wanda Ustaz Zakariyya Ajiya ya wakilta, ya gode wa kwamitin gudanarwar taron kan […]

kungiyar Izala ta yi wa malaman tafsiri taron bita a Gombe

Alhaji Salisu Muhammad Gombekungiyar Jamaátu Izalatil bidiá wa íkamatissunnah ta kasa, reshen Jihar Gombe ta gudanar da taron bita, a cibiyar ilmi, ga malamai da limamanta kafin su fara gudanar da tafsirai na bana a jihar.
A jawabinsa, shugaban kungiyar na jiha, Alhaji Salisu Muhammad Gombe, wanda Ustaz Zakariyya Ajiya ya wakilta, ya gode wa kwamitin gudanarwar taron kan yadda komai ya gudana cikin nasara. Sai kuma ya tunatar da malaman kan su isar da sakon Allah, kamar yadda Manzon Allah (SAW) ya karantar. Ya bukaci alúmmar jihar su yawaita adduó’in dorewar zaman lafiya a jihar da kuma kasa baki daya.
Daga nan ya nemi mawadata su ribanci wannan wata wajen kara taimaka wa gajiyayyu da marasa galihu.
Shi kuwa Sheikh Usman Isa Taliyawa jan hankalin malaman ya yi su bi shariá wurin hada kan alúmma ta fuskar hikima a tafsirinsu ta yadda, daga karshe bukata zata biya.
Farfesa Umar Labdo na Jamiár Bayero Kano, shi tsokaci ya yi kan Musulmi su guje wa miyagun akidu da ke ruguza imani da gurbata tarbiyya da zamantakewar dan Adam.
Shi ma Dokta Ahmad Abdullahi Ash-shaáli, jawabi ya gabatar kan sharuddan gudanar da tafsiri, wadanda wajibi malaman su fahimce su saboda kauce wa aikata kura-kurai, irin yadda wasu malamai ke tafkawa a lokacin tafsiransu.
Haka nan Dokta Rasheed Abdulganiy, na jamiár jihar ta Gombe tsokaci ya yi kan irin muámalar da mai gudanar da tafsiri zai yi da kowane darasin da yake son gabatarwa, domin tasirantuwar karantar da mutane.
A jawabin rufe taro, mataimakin shugaban majalisar malamai na jiha, Iman Abubakar Lamido ya gode wa malaman kan yadda kowanensu ya gabatar da kasidarsa, kuma ya bukaci mahalarta taron su yi amfani da abubuwan da suka koya a bitar.