kungiyar Izala ta yi wa shugabanni bitar sanin makamar aiki
kungiyar Jama’atu Izalatil Bid’ah Wa Ikamatis Sunnah (JIBWIS) ta kasa, reshen karamar Hukumar Jos ta Arewa da ke Jihar Filato, ta gudanar da taron bita ga shugabannin rassanta da kwamitocin masallatai, kan sanin makamar aiki.Da yake jawabi a wajen taron, wanda aka gudanar a masallacin ’Yan Shanu da ke garin Jos, shugaban majalisar malamai na […]
kungiyar Jama’atu Izalatil Bid’ah Wa Ikamatis Sunnah (JIBWIS) ta kasa, reshen karamar Hukumar Jos ta Arewa da ke Jihar Filato, ta gudanar da taron bita ga shugabannin rassanta da kwamitocin masallatai, kan sanin makamar aiki.
Da yake jawabi a wajen taron, wanda aka gudanar a masallacin ’Yan Shanu da ke garin Jos, shugaban majalisar malamai na kungiyar, reshen jihar, Dokta Hassan Abubakar Dikko ya yi na’am da taron, inda ya nuna a dora mutane kan sanin makamar aiki, ba karamin al’amari ba ne.
Ya ce za a sami gagarumar nasara idan dukkan rassan kungiyar na kananan hukumomin jihar suka gudanar da irin wannan taro, “Karantar da shugabanni sanin makamar aiki ya zama wajibi, saboda haka ina kira ga dukkan shugabannin kungiya su yi aiki don Allah, kuma su yi karatu, domin karatun nan shi ne zai taimaka mana mu zamanto masu tsaron Allah, mu yi don Allah kuma mu zamanto masu hangen nesa”. Inji shi.
A nasa jawabin, shugaban majalisar malaman reshen, Ustaz Muhammad Haris Shehu ya bayyana sun shirya taron ne sakamakon umarnin da shugaban majalisar malamai na jihar, Dokta Hassan Abubakar Dikko, ya bayar, saboda haka ya yi kira ga wadanda suka halarci taron su yada abubuwan da aka karantar da su.