Kungiyar JOHESU ta yi zanga-zanga kan rashin biyan albashi

Kungiyar Ma’aikatan Lafiya ta Kasa (JOHESU) reshen Jihar Kano ta gudanar da zanga-zangar lumana ta wuni uku don nuna rashin jin dadinta kan abin da ta kira rashin biyan albashi ga ’ya’yanta.                                                                                                                                          Shugaban kungiyar Kwamared Harisu Hamza ya ce, sun shirya  zanga-zangar ce don jawo hankalin jama’a kan halin ha’ula’in da suke ciki na rashin […]

Kungiyar JOHESU ta yi zanga-zanga kan rashin biyan albashi
Kungiyar JOHESU ta yi zanga-zanga kan rashin biyan albashi

Kungiyar Ma’aikatan Lafiya ta Kasa (JOHESU) reshen Jihar Kano ta gudanar da zanga-zangar lumana ta wuni uku don nuna rashin jin dadinta kan abin da ta kira rashin biyan albashi ga ’ya’yanta.                                                                                                                                          Shugaban kungiyar Kwamared Harisu Hamza ya ce, sun shirya  zanga-zangar ce don jawo hankalin jama’a kan halin ha’ula’in da suke ciki na rashin samun albashinsu na wasu watanni.

Kwamared Harisu ya bayyana cewa ba kawai wulakanta harkar lafiya Gwamnatin Tarayyar ta yi ba a gefe daya kuma gwamnatin ta yi watsi da umarnin kotu wacce ta yanke hukuncin cewa a biya ma’aikatan lafiyar.

“Wannan ya nuna gwamnati ba ta girmama umarnin kotu domin ita ta yi umarnin a biya mu bashin albashin da muke bin Gwamnatin Tarayya haka kuma kotun ta umarci gwamnatin ta tabbatar da yin gyaran albashinmu a kan tsarin ‘CONHESS.’

Kwamared Harisu ya kara da cewa, lura da muhimmancin da kiwon lafiya ke da shi bai kamata gwamnati ta yi wasa da shi ba, don haka kungiyar ta yi kira ga gwamnati ta gaggauta biya musu bukatunsu kafin kungiyar ta dauki mataki na gaba.