kungiyar kabilar Ibo Musulmi ta ziyarci Etsu Nupe

Shugaban kungiyar kabilar Ibo Musulmi da ke Jihar Neja, Malam Suleiman Muhammad Ayogu ya bayyana yadda kabilar Ibo ne ke kara rungumar addinin Musulunci, musamman a wannan lokacin da ake yawan nuna wa addinin kiyayya da kyama da wariya.Malam Suleiman ya sanar da haka ne lokacin da ya jagoranci tawagar da ta kai wa Mai […]

kungiyar kabilar Ibo Musulmi ta ziyarci Etsu Nupe
kungiyar kabilar Ibo Musulmi ta ziyarci Etsu Nupe

Shugaban kungiyar kabilar Ibo Musulmi da ke Jihar Neja, Malam Suleiman Muhammad Ayogu ya bayyana yadda kabilar Ibo ne ke kara rungumar addinin Musulunci, musamman a wannan lokacin da ake yawan nuna wa addinin kiyayya da kyama da wariya.
Malam Suleiman ya sanar da haka ne lokacin da ya jagoranci tawagar da ta kai wa Mai Martaba Etsu Nupe kuma Shugaban Majalisar Sarakunan Jihar Neja, Alhaji Yahaya Abubakar ziyara a fadarsa  da ke Bidda.
Shugaban ya bayyana cewa akasarin wadanda ke musulunta sukan dauki lokaci suna bincike game da yadda addinin Islama yake ta fuskar karanta littattafan addinin, lamarin da a karshe kan kai su ga kama addinin gadan-gadan.
Da yake tsokaci dangane da musuluntar A’isha, Malam Suleiman, ya ce bai kamata ya tayar da kurar da ya tayar ba, idan aka yi la’akari da kundin tsarin mulkin kasar nan da ya ba kowa damar yin addinin da yake sha’awa. “Babban abin da ke daure mini kai shi ne idan musulmi ya koma addinin Kirista, babu wanda ke daga harshe a kan hakan, sai dai kiristoci kan yi taron dangi a duk lokacin da kirista ya rungumi addinin musulunci”. Inji shi.
Ya jinjina wa Mai Martaba Etsu Nupe game da yadda ya tafiyar da lamarin, a matsayinsa na uban al’umma, duk da irin kashin kajin da aka yi ta shafa masa a kafofin watsa labarai daban-daban da ke fadin kasar nan.Ya jaddada cewar a matsayinsu na wadanda ke da jama’a a masarautarsa, suna da labarin irin ayyukan ciyar da yankinsa gaba da yake yi tun daga lokacin da ya zama Etsu Nupe.
A jawabinsa, Mai Martaba Etsu Nupe, Alhaji Yahaya Abubakar ya danganta al’amarin A’isha da kaddarar Allah, Wanda Ya tsara duk abubuwan da za su faru a kan bayinSa daga farko har karshe.
Ya ce a matsayinsa na jagoran jama’arsa ba zai bari wani daga cikinsu ya tagayyara ba, “Shi ya sa na dauki matakan ba kowa hakkinsa gwargwadon iko, kuma, Ahamdulillahi, Allah Ya sa kungiyar Kiristoci ta Najeriya (CAN) ta fahimci gaskiyar lamarin da yadda Sakatarenta na kasa, Rabaren Musa Asake ya wanke zarge-zargen da Pastor Raymond ya yi na an tilasta wa ’yarsa musulunci da boye ta a fada,tare da hana shi ganinta”. Inji shi.
Ya yi na’am da ziyarar da tawagar ta kawo masa, ya sa musu albarka, kuma ya ce wannan wani mataki ne na kara inganta dangantaka tsakanin jama’ar Inyamurai da masarautarsa, musamman ganin cewar suna bayar da gagarumar gudunmuwa wurin ciyar da Masarautarsa gaba da ma duk wuraren da suka gudanar da al’amuransu na yau da kullum.