Kungiyar Kansiloli ta Jihar Yobe ta ba dan takarar Gwamna gudumawar motoci

A lokacin da ake shirye-shiryen zaben Gwamna da Majalisar Dokoki, Kungiyar Kansilolin Jihar Yobe (Yobe Councillors Forum) ta kashe fiye da Naira miliyan uku wajen ba dan takarar Gwamna da sauransu gudunmawar motocin kamfe. Da take zantawa da Aminiya a Damaturu bayan mika makullan motocin, Shugabar Kungiyar Hajiya Hafsat Alhaji Ado, Kansila mai wakiltar  Damaturu ta […]

Kungiyar Kansiloli ta Jihar Yobe ta ba dan takarar Gwamna gudumawar motoci
Kungiyar Kansiloli ta Jihar Yobe ta ba dan takarar Gwamna gudumawar motoci

A lokacin da ake shirye-shiryen zaben Gwamna da Majalisar Dokoki, Kungiyar Kansilolin Jihar Yobe (Yobe Councillors Forum) ta kashe fiye da Naira miliyan uku wajen ba dan takarar Gwamna da sauransu gudunmawar motocin kamfe.

Da take zantawa da Aminiya a Damaturu bayan mika makullan motocin, Shugabar Kungiyar Hajiya Hafsat Alhaji Ado, Kansila mai wakiltar  Damaturu ta Tsakiya ta ce wannan ne karo na farko da kungiyar ta bayar da irin wannan gudunmawa.

“Mun yi wannan kokari ne saboda yadda Gwamna Ibrahim Gaidam yake kyautata mana shi ya sa muka sayi motoci  biyu kirar Honda Cibic da Carina E muka ba wa Gwamna mai jiran gado Alhaji Mai Mala Buni don yakin neman zaben da sauran ’yan takara,” inji ta.