kungiyar kare hakkin mata na horar da karuwai yadda ake tantance jabun kudi
Wata kungiyar kare hakkin mata ta Indomitable women da ke kasar Indiya, ta fara bai wa karuwai horo kan yadda za su tantance jabun kudi, a garuruwan Kolkata da Sonagachi, inda a kalla ake da mata masu zaman kansu da yawansu ya kai dubu takwas.kungiyar matan ta bullo da shirin horarwar ne bayan da aka […]
Wata kungiyar kare hakkin mata ta Indomitable women da ke kasar Indiya, ta fara bai wa karuwai horo kan yadda za su tantance jabun kudi, a garuruwan Kolkata da Sonagachi, inda a kalla ake da mata masu zaman kansu da yawansu ya kai dubu takwas.
kungiyar matan ta bullo da shirin horarwar ne bayan da aka yi ta cutar karuwan kasar, kuma idan sun kai kara ba za a bi kadin hakkinsu ba, domin karuwanci babban laifi ne a kasar Indiya. Smarajit Jena, Babbar mai bayar da shawara ga kungiyar, ta ce: “Mafi yawan mata ba su da masaniya sun karbi jabun kudi, sai sun je banki don adana kudinsu.”
Sumanjir Ray, daya daga cikin ’ya’yan kungiyar,ta bayyana cewa akwai kimanin jabun takardun kudi sama da dubu 500, wadanda darajarsu ta kai rupees miliyan 21 da aka kwace a sassa daban-daban na kasar.