kungiyar kasashen Larabawa ta goyi bayan Saudiyya a kan kin kujerar Majalisar dinkin Duniya

Shugaban kungiyar kasashen Larabawa ta “Arab League,” Nabil al-Arabi ya nuna goyon bayansa kan matsayin da kasar Saudiyya ta dauka na watsi da kujerar Majalisar Tsaro ta Majalisar dinkin duniya, inda ya nuni da cewa majalisar ta nuna gazawa kan al’amuran da suka shafi kasashen Larabawa.Arabi ya yi wa manema labarai karin bayani, inda ya […]

kungiyar kasashen Larabawa ta goyi bayan Saudiyya a kan kin kujerar Majalisar dinkin Duniya
kungiyar kasashen Larabawa ta goyi bayan Saudiyya a kan kin kujerar Majalisar dinkin Duniya

Shugaban kungiyar kasashen Larabawa ta “Arab League,” Nabil al-Arabi ya nuna goyon bayansa kan matsayin da kasar Saudiyya ta dauka na watsi da kujerar Majalisar Tsaro ta Majalisar dinkin duniya, inda ya nuni da cewa majalisar ta nuna gazawa kan al’amuran da suka shafi kasashen Larabawa.
Arabi ya yi wa manema labarai karin bayani, inda ya ce Saudiyya na da gaskiyar nufi, wajen yin watsi da wannan kujera, musamman in an yi la’akari da yadda majalisar ta nuna gazawa wajen tabbatar da zaman lafiya a duniya, “don babu wani aikin kwarai da take yi,” a cewarsa.
Ya ce kasashen Larabawa, wadanda suka hada da Falasdinu da Siriya, su suka fi shan wahala a sanadiyyar nakasun Majalisar Tsaro a shekaru 60 din da suka gabata.
kungiyar kasashen Musulmi ta OIC ta goyi bayan kasar Saudiyya, inda ta bayyanba kin amincewar Gwamnatin Riiyadh na kara kujerar a majalisar tsaro, da cewa “matakin zai haifar da sauye-sauyen yara ga Majalisar tsaron, ta yadda za a tabbatar da aiwatar da gaskiya keke da keke, da kuma samun cikakken wkailci.” Baban Sakataren kungiyar Hadin Kan kasashen Musulmin , Ekmeleddin Ihsanoglu, ya bayyana cewa, kungiyarsa da ’ya’yanta 57 na da bukatar kawo gyara a majalisar tsaro ta Majalisar dinkin Duniya.
Jakadan Saudiyya a Majalisar dinkin Duniya ya ragargaji Majalisar Tsaro, inda ya jajircewa kan cewa kasarsa na nan a kan bakanta na kin karbar kujerar da aka bata. Abdalla Al Mouallimi ya yi tur da da majalisar tsaro ta Majalisar dinkin Duniya kan gazawarta na shawo kan rikice-rikicen da ke tsakanin Isra’ila da Falasdinawa da kuma rikicin kasar Siriya; sannan ta kasa mayar da yankin Gabas ta Tsakiya ya zama inda ba a mu’amala da makaman nukiliya, musamman a tarurrukan da ta saba shiryawa kan al’amuran da suka shafi yankin.
A Juma’ar da ta gabata ne, Gwamnatin Saudiyyar ta yi watsi da matsayin da aka ba ta a  majalisar tsaron, bayan a zabeta a matsayi da ake bai wa wasu kasashe na shekaru biyu.
Al Mouallimi ya yi wa manema labarai nuni da cewa akwai yiwuwar gwamnatin kasarsa ta aike da takarda ga Majalisar dinkin Duniya ta hannun Ma’aikatar Harkokin Wajen, kamar yadda bayanai suka tabbatar.