Kungiyar kasashen Musulmai ta yi alla-wadai da hare-haren Isra’ila a Gaza

Kungiyar ta ce Isra’ila na aikata laifukan yaki a Gaza

Kungiyar kasashen Musulmai ta yi alla-wadai da hare-haren Isra’ila a Gaza

OIC

Kungiyar Kasashen Musulmai ta Duniya (OIC) a ranar Laraba ta yi alla-wadai da hare-haren da Isra’ila ta kaddamar a Zirin Gaza.

OIC ta kuma soki lamirin kasashen da suke goyon isra’ilar a daidai lokacin da Shugaban Amurka, Joe Biden yake ziyara a kasar.

Kungiyar, a cikin wata sanarwa da ta fitar bayan kammala taron Ministocin Harkokin Wajen Kasashe mambobinta ta kuma zargi Isra’ila da kai hari a kan asibitin Al-Ahli a ranar Talata, inda ta kashe sama da mutum 471 a Zirin na Gaza.

Kasashen Larabawa ma a daidaikunsu sun yi alla-wadai da harin na Isra’ila wanda ya yamutsa hazo a yankin Gabas ta Tsakiya.

To sai dai a yayin da yake ganawa da Firaminin Isra’ila, Benjamin Netanyahu a ranar Laraba, Shugaba Biden ya bayyana goyon bayan kasar shi ga Isra’ila cewa wani makamin roka da ’yan ta’adda suka jefa ne ya yi kuskure ya fada kan asibitin.

Bugu da kari, kungiyar ta OIC ta kuma soki lamirin Majalisar dinkin Duniya saboda ta ki tsawatarwa a daina yakin. (AFP)

 

Kotu ta yanke wa mutum 5 hukuncin rataya a Kano

NAJERIYA A YAU: Hanyoyin Noma Ba Tare Da Kashe Kuɗi Da Yawa Ba

HOTUNA: Hatsarin tirela ya yi ajalin mutum 4, shanu 15 da awaki 20 a Neja

Mai gari ya tsere bayan mazauna sun cinna wa gidansa wuta a Kano