Kungiyar Kasashen Musulumi na babban taro kan ta’addanci
Babban Taron OIC zai tattauna kan ta’addanci da tsangwamar Musulmai
Kungiyar Kasashen Musulmai (OIC) na gudanar da babban taronta karo na 47 wanda Jamhuriyar Nijar ta karbi bakunci.
Taron zai tattauna kan matsalolin da ke addabar mambobin OIC da kasashen da Musulumi ba su da rinjaye da kuma rikikcin yankin Sahel.
Tattaunawar za ta mayar da hankali ne kan lamurran da suka shafi ta’addanci, tsattsauran ra’ayi da kuma kyama da ake nuna wa Musulmai.
Sauran batutuwan da taron zai tattauna sun hada batun agaji ga al’ummomin da ke zaune yankunan da ake cikin tashin hankali.
Kasashen Musulmi 54 ne ke halartar taron bisa wakilcin ministocinsu na harkokin kasashen waje.
Minista a Ma’aikatar Harkokin Waje ta Najeriya, Ambasa Zubairu Dada ne ke jagorantar tawagar kasr a taron, wanda Shugaban Jamhuriyar Nihar, ke Mai Masaukin Baki.