Kungiyar Katsinawa da Daurawa mazauna Legas ta shirya addu’o’i kan zaben gobe

A yayin da ake shirin gudanar da zaben gwamnoni da na majalisun jihohi a gobe Asabar, a Jihar Legas, Kungiyar Katsinawa da Daurawa mazauna Legas ta shirya addu’o’i na musamman domin murnar nasarar Shugaba Buhari tare da godiya ga Allah, kan yadda aka gudanar da zabe lafiya da kuma fatan Allah Ya sa a yi na […]

Kungiyar Katsinawa da Daurawa mazauna Legas ta shirya addu’o’i kan zaben gobe

A yayin da ake shirin gudanar da zaben gwamnoni da na majalisun jihohi a gobe Asabar, a Jihar Legas, Kungiyar Katsinawa da Daurawa mazauna Legas ta shirya addu’o’i na musamman domin murnar nasarar Shugaba Buhari tare da godiya ga Allah, kan yadda aka gudanar da zabe lafiya da kuma fatan Allah Ya sa a yi na gobe lami lafiya a daukacin kasar nan.

Sakataren Kungiyar Katsinawa da Daurwa, Kwamared Kabir Musa ya shaida wa Aminiya cewa sun shirya addu’o’in ne domin addu’a ce maganin komai.  “Mun kuma yi ne domin nuna godiyarmu ga Allah Madaukakin Sarki da Ya bai wa Shugaba Buhari nasara, inda aka yi zaben lafiya don haka muna tawassuli da wadannan addu’o’in, Allah Ya sa yadda aka yi zaben Shugaban Kasa da na Majalisun Tarayya lafiya, a yi na gwamnoni da na majalisu jihohi ma lafiya. Wannan shi ne dalilin da ya sanya wannan kungiya ta gayyato malamai da shugabannin jama’a sa suka hada da sarakuna da sauran jama’a; muka hadu muka yi addu’a. Dama abin da muka saba yi ne, a lokacin da Shugaba Buhari ya fita jinya ma mun yi irin wannan addu’a, to yanzu Allah Ya karbi addu’armu, Ya ba shi lafiya sannan Ya ba shi jan ragamar kasar nan a karo na biyu. To, ai ka ga dole ne mu yi addu’ar godiya ga Allah tare da neman kariyarSa da nasararSa ga Shugaban Kasa Muhammadu Buhari,” inji shi.

Ya kara da cewa za su ci gaba da wayar wa jama’a kai domin su fito kwansu da kwarkwata su yi zaben gwamnoni da na  majalisun jihohi. Ya ce za su tabbatar mambobin kungiyarsu da suka karbi katin zabe a Legas sun fito sun yi zabe a Legas, sannan wadanda suka yi rajista a gida Katsina amma suke zaune a Legas, kungiyar za ta tallafa musu domin su tafi gida su yi zaben a can.

“Mun fito da tsarin tallafa wa marasa karfi a cikinmu wadanda suka yi rajistar zabensu a Jihar Katsina domin su je gida su yi zaben a can. Ka san cewa da yawansu sun dawo Legas bayan da suka je gida suka yi zaben Shugaban Kasa,” inji shi

A karshe ya yi kira ga matasa su guji bangar siyasa, kuma kada su yarda wadansu su yi amfani da su wajen tayar da hankalin jama’a a zaben na gobe. “In ka lura, babu wani abin da ke tabbata sai da zaman lafiya. Shi kansa shugabancin ana yin sa ne yadda ya kamata idan kasa na zaune lafiya. Don haka fatarmu a zauna lafiya,” inji shi.

A wani labarin ’yan kasuwar gwangwan da ke Ojota a Legas, baya ga addu’ar da suka shirya, sun gabatar da biki na musamman, inda aka shirya wasannin gargajiya da kade-kade da raye-raye saboda murnar lashe zaben da Shugaba Buhari ya yi. Wasannin gargajiyar da aka shirya sun hada da wasan dambe da na barkwanci, inda makada da dama na ’yan Arewa mazauna Legas, suka baje kolinsu a wurin bikin.

Alhaji Ibrahim Soja Sarkin ’Yan Gwangwan na jihohin Yamma shi ya jagoranci bikin. Ya shaida wa Aminiya cewa sun dade suna fata tare da shirya addu’o’i domin ganin Shugaba Buhari ya yi nasara. “Bayan da Allah Ya tabbatar mana da wannan nasara sai na gayyato ’yan uwa da abokan arziki domin su zo mu yi murnar wannan nasara da Allah Ya bai wa Shugaba Buhari tare da yin addu’ar Allah Ya tabbatar mana da alheri a shekaruahudun da zai yi na mulkinsa,” inji shi.

Ya ce akwai bukatar jama’a su fito kwansu da kwarkwata a zabubbukan da za a yi gobe domin a zaben Shugaban Kasa jama’a da dama ba su fito zaben ba. “Zan so in fadi da babbar murya, mu a nan Legas ’yan Arewa sun fito yadda ya kamata sun yi zaben Shugaban Kasa haka ma al’ummar Ibo su ma sun fito zabe amma a gaskiya Yarbawa ba su fito ba. Ni ban san abin da ya hana su ba, ban san ko me suke tsoro ba amma ba su fito ba. Don haka ina kira ga duk ’yan Najeriya da ke da katin zabe da ’yan Arewa da Yarbawa da al’ummar Ibo kowa ya fito ya yi zaben gwamnoni da na wakilan majalisun jihohi domin katin zabe shi ne karfin talaka, shi ne makaminsa. Da shi talaka yake samun ’yancinsa, don haka ban ga dalilin da zai sa mutum ya ki fitowa neman ’yancinsa a lokacin da yake da damar yin haka ba,” inji shi.

Bikin murnar zaben ya gudana lafiya a Kasuwar ’Yan Gwangwan da ke Gidan Kwali a Ojota da sauran sassan Legas da dama da aka shirya bukukuwa.