kungiyar Katsinawa da Daurawa ta bai wa marayu tallafi a Kebbi
kungiyar Katsinawa da Daurawa mazauna Jihar Kebbi ta kai tallafi kayan masarufi gidan marayu da ke Birnin- Kebbi, kwanakin baya. A lokacin ziyarar Shugaban kungiyar Alhaji Bashir Sulaiman Gaci ya bayyana cewa kungiyarsu ta yanke shawarar kawo kayan tallafin ga marayun ne domin kara rage masu radadin rashin iyaye da kuma inganta rayuwarsu.Kayayyakin da kungiyar […]
kungiyar Katsinawa da Daurawa mazauna Jihar Kebbi ta kai tallafi kayan masarufi gidan marayu da ke Birnin- Kebbi, kwanakin baya.
A lokacin ziyarar Shugaban kungiyar Alhaji Bashir Sulaiman Gaci ya bayyana cewa kungiyarsu ta yanke shawarar kawo kayan tallafin ga marayun ne domin kara rage masu radadin rashin iyaye da kuma inganta rayuwarsu.
Kayayyakin da kungiyar ta kaiwa marayun sun hada da shinkafa da sabulai da butoci da kuma magungunan sauro.
A lokacin da take jawabi mai kula da gidan marayun Malama Hassana Hussaini Warra ta jinjina wa kungiyar. Ta ce idan ana samun irin wadannan kungiyoyin masu tallafawa marayu, lalle za su rage wa gwamnati nauyin wadansu ayyuka.
A karshe ta yi kira ga sauran kungiyoyi da su yi koyi da kungiyar.