kungiyar ‘Ki Gyara Da Kanki’ ta ciri tuta

kungiyar Ki Gyara Da Kanki ta bayyana cewa ta shirya tsaf wajen yin tafiya tare da maza don ganin rayuwar aure ta inganta. Hajiya Aisha Ibrahim Isah ita ce shugabar kungiyar, ta bayyana cewa kungiyar tasu wacce ta dauki tsawon shekaru 13, an kafa ta ne da niyyar gyaran zamantakewar aure da iyali. Ta bayyana […]

kungiyar ‘Ki Gyara Da Kanki’ ta ciri tuta

kungiyar Ki Gyara Da Kanki ta bayyana cewa ta shirya tsaf wajen yin tafiya tare da maza don ganin rayuwar aure ta inganta. Hajiya Aisha Ibrahim Isah ita ce shugabar kungiyar, ta bayyana cewa kungiyar tasu wacce ta dauki tsawon shekaru 13, an kafa ta ne da niyyar gyaran zamantakewar aure da iyali.

Ta bayyana cewa kungiyar tana gudanar da ayyukanta ne ta hanyar shirya bitoci ga matan aure har ma da zawarawa da ‘yan mata inda suke gayyato kwararru daga fagage na rayuwa daban-daban suna ba mata bita akan yadda za su zauna da mazajensu da kuma yadda za su yi kwalliya da gyaran jiki da iya girki da sauransu.

Hajiya Aisha ta bayyana cewa baya ga shirya bitoci ga mata wajen

zamantakewar iyali da kungiyar tasu ke yi, har ila yau su kan koya wa matan sana’o’i ta yadda za su sami abin dogaro da kansu. “Bayan mun koya wa matan nan yadda za su zauna da mazajensu ta hanyar ladabi da biyayya da iya magana da tsafta da kwalliya da gyaran jiki, haka kuma muna koya musu sana’oi ta yadda za su zama masu tallafa wa mazajensu da ‘ya’yansu daga dan kwabo da sisi da ke shigowa hannunsu, ma’ana yadda za su zama masu dogaro da kansu.”

Shugabar kungiyar ta kara da cewa matan da ke karkara ma ba a bar su a baya waje cin moriyar kungiyar ba, domin a cewarta kungiyar takan shiga har cikin kauyika don shirya wa matan irin wadanann bitoci inda kuma suke nema wa matan tallafin jari daga masu arzikin da ke yankunansu, “Ba a cikin Kano kawai muke yin ayyukanmu ba, mukan shiga har cikin kauyuka mu gudanar da irin wadancan bitoci inda a karshe idan muka gama mu su bitar mukan nema musu tallafi daga masu hannu da shuni na garin don ba su abin da za su yi jari da shi. Misali a kwanakin baya mun yi irin haka a karamar Hukumar Rano inda muka nemi A.A. Rano da ya taimaka musu da jari kuma cikin nasara ya amsa rokonmu ya ba su tuni yanzu matan sun sami riba biyu ga ta gyaran zamantakewa ga kuma ta sana’a.”

A cewarta ba za ta iya kirga auren da suka daidaita ta hanyar taimakon kungiyarsu ba, domin a lokuta da dama mazaje kan zo su yi musu godiya sakamkon canjin zamantakewa kyakkyawa da suka samu daga matayensu bayan sun halarci ire-iren bitocin da kungiyar ke shiryawa. Sannan sai ta yi kira ga gwamnati da musu hannu da shuni da su shigo su tallafa wa kungiyar ganin cewa ayyukansu na gyaran zamantakewar iyali ne gaba daya ganin cewa sai iyali sun daidaitu sannn za a samu nagartacciyar al’umma a kasa, domin ayyukan da muke yi yawanci na bukatar kudi musamman sha’anin koyar da sana’o’i.