Kungiyar Kiristoci ta bukaci a yi bincike kan rushewar masallaci a Zariya
Kungiyar ta ce yin hakan zai kare aukuwar lamarin a nan gaba
Kungiyar Kiristoci ta Najeriya (CAN) ta bukaci Gwamnatin Tarayya da ta Jihar Kaduna da su gudanar da zuzzurfan bincike kan musabbabin rushewar ginin masallacin Fadar Sarkin Zazzau.
A ranar Juma’ar sa ta gabata ne dai wani sashe na ginin babban masallacin wanda ke kofar fada ya rushe ana tsaka da sallar La’asar, inda ya kashe mutum 10, wasu da dama kuma suka jikkata.
Shugaban na CAN na kasa, Achbishop Daniel Okoh, ne ya yi kiran a cikin sakonsa na jaje ga al’ummar musulmin Zariya.
A cikin sanarwar da ya fitar a Abuja, Daniel ya ce yin binciken ne zai a a kaucewa sake aukuwar hakan a nan gaba.
Ya kuma yi kira ga gwamnatoci da su tashi tsaye wajen tabbatar da lafiya da tsaron wuraren ibada a Najeriya.
Shugaban Kiristocin ya ce ya kadu matuka da jin labarin rushewar ginin da ma na mutuwar mutanen, inda ya roki Allah Ya yi musu gafara Ya kuma ba iyalansu hakurin jure rashinsu.
Ya kuma yaba wa jami’an hukumomi da kungiyoyin bayar da agajin gaggawa saboda yadda suka yi saurin kai dauki a wajen da lamarin ya faru.