Kungiyar kwadago na yunkurin komawa yajin aiki
Kungiyar kwadago ta kasa NLC ta zargi gwamnatin tarayya da kawo rudani akan yarjejeniyar da suka kulla geme da mafi karancin albashi ga ma’aikatan kasar. Hakan yasa kungiyar take yunkurin komawa yajin aiki a ranar 6 ga Nuwamba 2018. A wata sanarwa da Shugaban NLC na kasa Mista Ayuba Wabba ya rattaba wa hannu da […]
Kungiyar kwadago ta kasa NLC ta zargi gwamnatin tarayya da kawo rudani akan yarjejeniyar da suka kulla geme da mafi karancin albashi ga ma’aikatan kasar. Hakan yasa kungiyar take yunkurin komawa yajin aiki a ranar 6 ga Nuwamba 2018.
A wata sanarwa da Shugaban NLC na kasa Mista Ayuba Wabba ya rattaba wa hannu da shugaban kungiyar ‘yan kasuwa Mista Joe Ajaero sun ce, ba gaskiya ba ne cewa kungiyar ta bukaci gwamnatin tarayya da ta biya naira dubu 30 a matsayin albashi mafi karanci.