kungiyar kwallon guragu ta koka da rashin samun tallafi

Mai horar da kungiyar kwallon guragu dake Layin Bagobiri a  Unguwar Hausawa  Kalaba da ke Jihar Kuros Riba, Abubakar Salihu ya  bayyana babbar matsalar da kungiyarsa take fuskanta na rashin samun wanda zai dauki nauyin  kungiyar da kuma kula da ita yadda ya dace.  Ya ce kungiyar tana da zaratan ’yan kwallon da suke buga […]

kungiyar kwallon guragu ta koka da rashin samun tallafi
kungiyar kwallon guragu ta koka da rashin samun tallafi

Mai horar da kungiyar kwallon guragu dake Layin Bagobiri a  Unguwar Hausawa  Kalaba da ke Jihar Kuros Riba, Abubakar Salihu ya  bayyana babbar matsalar da kungiyarsa take fuskanta na rashin samun wanda zai dauki nauyin  kungiyar da kuma kula da ita yadda ya dace.  
Ya ce kungiyar tana da zaratan ’yan kwallon da suke buga wa kungiyoyin kwallon guragu a  Jihohin Bayelsa da Ribas wasa a shekarun baya, amma abin bakin ciki yanzu sun koma Kuros Riba babu wanda ya nuna sha’awar daukar nauyin kungiyar a  matakin gwamnatin jiha ko kuma daga wata jiha a Arewacin Najeriya.
Shugaban ya fadi  haka ne yayin hira da Aminiya a Kalaba.   Ya ce babbar matsalar da ta fi damun kungiyar su ita ce ta rashin samun wanda zai dauki nauyin kungiyar a Kuros Riba ko kuma daga Arewa.
Malam  Salihu ya kara da cewa suna fuskantar matsalar kayayyakin wasa da suka hada da takalma da riguna da kuma takamaiman filin atisaye da isassun magungunan da dan wasa idan ya ji ciwo za a kula da shi.
Ya ce babban burinsu shi ne samun wanda zai dauki nauyin kungiyar walau a matakin gwamnati ko a daidaikun mutane.
Ya kara da cewa “yan wasan sun taba lashewa Jihohin Bayelsa da Kuros Riba lambobin yabo a wasanni daban-daban da suka halarta a baya, kuma yanzu haka wasu daga cikin su sun shirya tafiya Jihar Kano don halartar wasannin motsa jiki da Gwamnan Kano Alhaji Abdullahi Ganduje  da Mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Muhammadu Sanusi na biyu suka shirya a watan gobe ciki har da  wasan kwallon guragu.

Boko Haram sun ƙone makarantu a Borno

Har yanzu ’yan bindiga ba su saki matar Manjo Janar Rabe ba

An binne gawar Manjo Janar Rabe a Katsina

Wasu tsiraru ne ke rura matsalar tsaro a Najeriya — Christopher Musa