Kungiyar kwallon kafa ta Al-Nassr ta fara zawarcin Kante
Dan wasan ya rasa gurbin zuwa Gasar Kofin Duniya sakamakon rauni da ya ji.
Kungiyar kwallon kafa ta Al-Nassr da ke kasar Saudiyya ta shiga zawarcin dan wasan Chelsea, Ngolo Kante.
Kwantaragin Kante zai kare da Chelsea a karshen kakar wasanni ta 2022, kuma kungiyar ba ta da ra’ayin sabunta kwantaragin dan wasan tsakiyar.
Kante dai ya rasa gurbin zuwa Gasar Cin Kofin Duniya da aka kammala a Qatar sakamakon raunin da yake fama da shi.
Tsohon dan wasan na kungiyar kwallon kafa ta Leicester City, ba zai dawo murza leda ba sai Fabrairun 2023, amma hakan bai hana kungiyoyi fara zawarcinsa ba.
Duk da kungiyoyi da yawa da suka fara zawarcin Kante, amma ana tunanin Al-Nassr za ta iya daukar dan wasan duba da irin kudin da kungiyar ke shirin narkawa don daukarsa.
Jaridar Foot Mercato, ta rawaito cewar Al-Nassr ta shirya daukar dan wasan kafin kakar wasanni mai zuwa.
A baya-bayan nan, Al-Nassr ta zuba kudi masu yawa don daukar tsohon dan wasan Manchester United, Cristiano Ronaldo, bayan warware kwantaraginsa da kungiyar.