kungiyar kwallon kafa ta mata ta lallasa ta ’yan jarida ta maza

kungiyar kwallon kafa ta mata ta lallasa ta ’yan jarida ta maza… Masu iya magana sun ce duk abin da maza za su yi mata za su iya yin fiye da hakas. A makon da ya gabata ne kungiyar kwallon kafa ta matan Jihar Nasarawa da aka fi sani da Amazon FC ta lallasa kungiyar […]

kungiyar kwallon kafa ta mata ta lallasa ta ’yan jarida ta maza
kungiyar kwallon kafa ta mata ta lallasa ta ’yan jarida ta maza

kungiyar kwallon kafa ta mata ta lallasa ta ’yan jarida ta maza…

Masu iya magana sun ce duk abin da maza za su yi mata za su iya yin fiye da hakas. A makon da ya gabata ne kungiyar kwallon kafa ta matan Jihar Nasarawa da aka fi sani da Amazon FC ta lallasa kungiyar kwallon kafa ta maza ta ’yan jarida ta Jihar Nasarawa da ake kira SWAN.

An yi wasan ne a ranar Asabar a filin wasa na Kwalejin Kimiyya da Fasaha na Jihar NasarawaWasan abuga shine a ranar Asabar da safe a filin wasa na Kwalajen na Jihar Nasarawa da ke garin lafia inda daruruwan ’yan kallo suka halarci filin ganin kungiyoyin kowa na ji da kansa.
’Yar wasan Amazon ce ta fara zura kwallo a ragar mai tsaron gidan kungiyar SWAN yayin da SWAN taa farke kwallon a cikin minti biyar tsakani.
Bayan da aka dawo daga hutun rabin lokaci ne sai kungiyar Amazon ta mata ta kara kwallo ta biyu da hakan ya sa aka tashi wasan da ci 2-1.
Duk da cewa wasu na ganin girma ya fadi wai rakumi ya shanye ruwan kaji amma mai horar da ’yan wasan Amazon ya ce ’yan wasansa ba su yi kokari ba duk da nasarar da suka samu a wasan saboda ba su taba samun nasara mafi da kwallaye mafi karanci kamar a wannan wasa ba. Ya ce ya yi tsammanin za su yi nasara a wasan da kwallaye da yawa amma sai ga shi da kayar suka zura wa kungiyar kwallon kafa ta Swan ta maza kwallaye biyu a raga da hakan ta sa aka tashi 2-1.