‘kungiyar Lafiya ta Duniya za ta gama rigakafin shan-inna a tsakiyar shekarar 2014’

Kungiyar  Lafiya ta Duniya (WHO) ta bayyana shirin kammala allurar rigakafin cutar shan-inna zuwa tsakiyar shekarar nan ta 2014.Dokta Adamu Ibrahim Ningi, babban jami’i mai lura da allurar rigakafin cutar a hukumar shi ne ya bayyana haka cikin hirarsa da wakilinmu a garin Alkaleri lokacin da ake gudanar da allurar. Ya ce yanzu ana samun […]

‘kungiyar Lafiya ta Duniya za ta gama rigakafin shan-inna a tsakiyar shekarar 2014’
‘kungiyar Lafiya ta Duniya za ta gama rigakafin shan-inna a tsakiyar shekarar 2014’

Kungiyar  Lafiya ta Duniya (WHO) ta bayyana shirin kammala allurar rigakafin cutar shan-inna zuwa tsakiyar shekarar nan ta 2014.
Dokta Adamu Ibrahim Ningi, babban jami’i mai lura da allurar rigakafin cutar a hukumar shi ne ya bayyana haka cikin hirarsa da wakilinmu a garin Alkaleri lokacin da ake gudanar da allurar.
Ya ce yanzu ana samun nasara yayin gudanar da allurar, idan an kwatanta da shekarun baya da ake samun matsalolin tirje wa shirin da wasu mutane ke yi, don a duk zagayen da ake yi mutane da kansu ke fito da yara don a diga musu. An samar da magunguna sama da milyan biyu, sannan akan zaburar da yaran ana ba su omo da sabulu da minti da sauransu.
Ya ce a tun shekarar 2000 ya kamata a kawar da cutar, amma bijirewar da mutane ke yi ta sa har yanzu ake yi. Kuma sama da watanni biyu ba a samu wani yaro mai dauke da cutar ba, tun daga biyar da aka samu a Bauchi, daya daga a Toro, ba a sake samun wani ba.
Dokta Ningi ya ce bayan an gama, za sanya cutar  kyanda da sankarau da bakon dauro da shawara da kuma sarkewar hakori, a gaba don kawar da su, kamar yadda aka kawar da kurkunu da agana da sauransu, kodayake tuni ana allurar rigakafin cututtukan.
Dokta Abubakar Duguri, babban jami’in lura da allurar rigakafin shan-inna na karamar Hukumar Alkaleri ya bayyana wa wakilinmu cewa an samu nasara a yankin, kuma an samar da shirin da ya dace tun da wuri, don haka mutane suna bayar da hadin kai yadda ya dace.

Matsalar Tsaro: Dole mu faɗakar da mutane yadda za su kare kansu – ACF

Majalisa ta buƙaci sojoji su kawo ƙarshen Lakurawa

Ɗan Aljeriya ya shiga hannu kan safarar makamai a Zamfara

’Yan bindiga sun kashe ’yan banga sun sace mai unguwa a Kaduna