Kungiyar Lauyoyi ta nesanta kanta daga yin karar Kwamishinan ’Yan sandan Kano

Kungiyar Lauyoyi ta Kasa reshen Jihar Kano ta nesanta kanta da batun da ake yadawa cewa, kungiyar ta yi karar Kwamishinan ’Yan sandan Jihar  Muhammad Wakili. A wata takarda da Sakataren Kungiyar Barista Mujitaba Adamu Amin ya sanya wa hannu kungiyar ta ce babu kanshin gaskiya a cikin wannan magana. Kungiyar ta ce, lauyan da […]

Kungiyar Lauyoyi ta nesanta kanta daga yin karar Kwamishinan ’Yan sandan Kano

Tsohon Kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar Kano Muhammad Wakili

Kungiyar Lauyoyi ta Kasa reshen Jihar Kano ta nesanta kanta da batun da ake yadawa cewa, kungiyar ta yi karar Kwamishinan ’Yan sandan Jihar  Muhammad Wakili.

A wata takarda da Sakataren Kungiyar Barista Mujitaba Adamu Amin ya sanya wa hannu kungiyar ta ce babu kanshin gaskiya a cikin wannan magana.

Kungiyar ta ce, lauyan da ya yi korafin shi ne Barista Muhammad Zubair kuma ba dan kungiyarsu ba ne.

Kungiyar ta ce, ba ta da wani dalili da zai sanya ta yi korafi a kan Kwamishinan ’Yan sandan Kano Muhammad Wakili . “Wancan lauya da ya yi wannan magana ya yi ta ce bisa radin kansa kuma ba dan kungiyarmu ba ne,” inji sanarwar.

A karshe kungiyar ta yi addu’ar neman samun dorewar zaman lafiya a Jihar Kano.

Rahotanni sun ce Barista Muhammad Zubair ya yi karar Kwamihinan ’Yan sandan Jihar Kano bisa zarginsa da kama Mataimakin Gwamnan Jihar, Dokta Nasiru Yusuf Gawuna bayan yana da masaniyar cewa, Mataimakin Gwamnan yana da rigar kariya wacce kundin mulkin Najeriya ya ba shi.

A ranar Lahadi 10 ga Maris ne ’yan sanda suka kama Dokta Nasiru Yusuf Gawuna tare da Kwamishinan Kananan Hukumomi na Jihar Kano Alhaji Murtala Sule Garo da Shugaban Karamar Hukumar Nasarawa Lamin Sani bisa zarginsu da kawo hargitsi a lokacin da ake tattara sakamakon zaben Karamar Hukumar Nasarawa.

Sai dai a wata ganawa da Rundunar ta ’Yan sandan ta yi da manema labarai ta ce, ba kama Mataimakin Gwamnan ta yi ba illa ta kubutar da shi ne daga cincinridon matasa da suka so su far masa wadanda kuma za su iya cutar da shi.