kungiyar Lawal Nuhu Kayarda ta fitar da wasu firsinoni daga gidan yarin Saminaka

kungiyar Lawal Nuhu Kayarda Forum da ke garin Saminaka a Jihar Kaduna, ta ’yanto wasu fursunoni biyu da suke gidan yarin Saminaka bayan ta biya tarar da aka yi musu a wani yanke hukunci da aka yi musu.Da yake jawabi a lokacin da yake karbar fursunonin, shugaban kungiyar, Alhaji Bala Isa, ya bayyana cewa sun […]

kungiyar Lawal Nuhu Kayarda ta fitar da wasu firsinoni daga gidan yarin Saminaka

kungiyar Lawal Nuhu Kayarda Forum da ke garin Saminaka a Jihar Kaduna, ta ’yanto wasu fursunoni biyu da suke gidan yarin Saminaka bayan ta biya tarar da aka yi musu a wani yanke hukunci da aka yi musu.
Da yake jawabi a lokacin da yake karbar fursunonin, shugaban kungiyar, Alhaji Bala Isa, ya bayyana cewa sun fitar da fursunonin ne saboda  nuna tausawa a gare su, ta hanyar biyan tarar da aka yi musu, musamman ganin laifin da suka yi bai taka kara ya karya ba.
Ya ce yin wannan yana daya daga cikin ayyukan kungiyar, saboda haka suka yi  fatar mutanen  su zama masu hali nagari, na kirki a gaba.
Alhaji Bala ya ce sun kafa kungiyar ce da sunan dan majalisar wakilai ta tarayya mai wakiltar mazabar Lere, Ibrahim Lawal Nuhu domin bayyana ayyukan da yake yi a mazabarsa da kuma taimaka wa al’umma da ya rika yi tun okacin da yake kwamishina da lokacin da yake shugabancin karamar Hukuma Lere.
Da yake jawabi a lokacin da yake mika farsinonin, babban jami’in gidan yarin Saminaka, Mista Gajere Yusuf ya bayyana lura da laifukansu bai taka kara ya karya ba,  ya sa aka ba kungiyar shawarar su biya tarar da aka yi musu. Don haka ya nuna farin ciki da kokarin kungiyar, kuma ya yi  fatar za ta cigaba da irin wannan aiki.

Matsalar Tsaro: Dole mu faɗakar da mutane yadda za su kare kansu – ACF

Majalisa ta buƙaci sojoji su kawo ƙarshen Lakurawa

Ɗan Aljeriya ya shiga hannu kan safarar makamai a Zamfara

’Yan bindiga sun kashe ’yan banga sun sace mai unguwa a Kaduna