Kungiyar Likitoci ta dakatar da yajin aiki bayan Shugaban Majalisar Wakilai ya shiga tsakani
Bayan shiga tsakani da Shugaban Majalisar Wakilai Femi Gbajabiamila ya yi, Kungiyar Likitoci ’Yan Kasa (NARD) ta dakatar da shiga yajin aikin da ta yi niyyar farawa. Kungiyar ta sanar da haka ne bayan Babban Taronta karo na 39 a Jihar Edo a watan Mayu cewa ta ba da wa’adin kwana 40 ko a biya […]
Bayan shiga tsakani da Shugaban Majalisar Wakilai Femi Gbajabiamila ya yi, Kungiyar Likitoci ’Yan Kasa (NARD) ta dakatar da shiga yajin aikin da ta yi niyyar farawa.
Kungiyar ta sanar da haka ne bayan Babban Taronta karo na 39 a Jihar Edo a watan Mayu cewa ta ba da wa’adin kwana 40 ko a biya basussukan da suke bin gwamnati, ko suka shiga yajin aikin sai baba ta gani.
Bayan wa’adin ya cika, sai Shugaban Majalisar Wakilai ya bukaci su dakatar da shirin da suke yi na shiga yajin aikin, sannan su ba shi lokaci domin ya nemo bakin zaren.
Shugaban kungiyar, Olusegun Olaopa ya ce sun dakatar da shiga yajin aikin ne domin su girmama bukatar da Shugaban Majalisar ya nema, sannan su ba shi dama ya gudanar da abin da ya yi niyya.