Kungiyar Likitocin Jihar Nasarawa tana horar da dillalan magunguna
Kungiwar Likitoci ta Jihar Nasarawa ta fara horar da dillalan magunguna kan hanyoyin inganta harkokinsu a jihar. A jawabinsa lokacin bude horarwar a Lafiya fadar jihar, Shugaban Kungiyar Dokta Nwora Okpakeake, ya ce horarwar na da manufar wayar da kawunan dillalan magunguna a jihar tare da samar musu hanyoyin gudanar da harkokinsu cikin ka’ida da […]
Kungiwar Likitoci ta Jihar Nasarawa ta fara horar da dillalan magunguna kan hanyoyin inganta harkokinsu a jihar. A jawabinsa lokacin bude horarwar a Lafiya fadar jihar, Shugaban Kungiyar Dokta Nwora Okpakeake, ya ce horarwar na da manufar wayar da kawunan dillalan magunguna a jihar tare da samar musu hanyoyin gudanar da harkokinsu cikin ka’ida da tsarin saye da sayar da magunguna a jihar da kasa baki daya.
Ya ce ya zame wa kungiyar dole ta tallafa wa kokarin da gwamnatotcin kasar nan yi wajen horar da masu sayar da magunguna a jihar musamman idan aka yi la’akari da kusantarsu da mazauna karkara don tabbatar da kare lafiyarsu.
A cewarsa a yayin horarwar wanda za a dauki sama da wata biyu ana yi za a mayar da hankali ne a fannonin gwaje-gwaje da suka hada da na ciwon maleriya da awon juna-biyu da tari da hawan jini da sauransu. Ya ce bayan horarwar, kungiyar za ta rika sa ido a harkokin masu harkar magunguna don tabbatar ba su kauce wa tsarin sana’ar ta zamani ba da sauransu. Ya bukaci mahalarta horarwar su yi amfani da abubuwan da za a koya musu don cimma burin shirin.
A vangaren Shugaban Kungiyar Dillalan Magunguna ta Jihar, Alhaji Abdulmalik Usman, ya yaba wa hangen nesa da Kungiyar Likitocin Jihar ta yi na shiryawa tare da gudanar da horarwar, inda ya ce ba shakka hakan zai taimaka wajen wayar da kawunan dillalan musamman a vangaren gudanar da sana’arsu yadda ya dace.
Horarwar ta samu halartar dillalan magunguna da dama da suka fito daga shiyyoyin jihar uku.