kungiyar ma’aikatan kotuna ta samu sababbin shugabanni
kungiyar ma’aikatan kotuna ta kasa, reshen Jihar Kebbi ta zabi sabbabin shugabanni, a wani taro da aka gudanar a babban dakin taro na Mai shari’a Balgore da ke babbar kotun shari’a a Birnin Kebbi.Sababbin shugabannin da aka zaba sun hada da Abdullahi Bala Alkali, a matsayin shugaba, sai Abubakar Zaki Mahe mataimakinsa; Samuel Amadi ya […]
kungiyar ma’aikatan kotuna ta kasa, reshen Jihar Kebbi ta zabi sabbabin shugabanni, a wani taro da aka gudanar a babban dakin taro na Mai shari’a Balgore da ke babbar kotun shari’a a Birnin Kebbi.
Sababbin shugabannin da aka zaba sun hada da Abdullahi Bala Alkali, a matsayin shugaba, sai Abubakar Zaki Mahe mataimakinsa; Samuel Amadi ya zama babban Sakatare, Malama Fati Garba kuma ta zama Ma’aji.
Kujerar mai bincike ta fada hannun Mustapha Mohammad Yusuf, yayin da Bashar Mohammad ya dare ta Sakataren Kudi, Abdullahi Aliyu Argungu kuma ya zama Sakataren tsare-tsare.
A jawabinsa bayan kammala zaben, shugaban kungiyar na kasa, Alhaji Mustapha Adamu ya ja hankalin shugabannin da su ji tsoron Allah, su rike amanar da aka damka musu. Kuma su kare mutuncin duk dan kungiya, musamman da yake a ma’aikatar shari’a nan ne tushen adalci yake.
Sannan ya ja hankalin’yan kungiya su ba shugabanni cikakken hadin kai da goyon baya, domin a sami kyakkyawar gudanarwa da ci gaba mai ma’ana.
Da yake godiya ga jama’ar da suka zabe su, sabon shugaban kungiyar ya nemi hadin kan kowane dan kungiya da ya ba da hadin kai da kuma kyawawan shawarwari da za su taimaka wajen ciyar da ita gaba, musamman ta fusakar inganta aikinsu.