Ma’aikatan majalisun jihohi sun janye yajin aiki
Wannan na zuwa ne bayan shafe makonni suna yajin aiki.
Kungiyar Ma’aikatan Majalisar Dokokin Jihohi (PASAN), ta janye yajin aikin da ta shiga na tsawon makonni.
Shugaban kungiyar reshen Jihar Gombe, Mohammad Bello Dukku, ya ce sun janye yajin aikin ne domin bai wa Gwamna Muhammad Inuwa Yahaya damar mika kasafi kudin jihar na shekarar 2024.
- Shugaban Majalisar Filato da mataimakinsa sun yi murabus
- Majalisa ta hargitse kan nadin sabbin shugabannin marasa rinjaye
A cikin wata sanarwa, Mohammad Bello Dukku, ya ce kungiyar ta sasanta tsakaninta da kwamitin ayyuka na kungiyar da kuma zauren kungiyar gwamnoni da masu ruwa da tsaki biyo bayan tattaunawar da suka yi.
Sanarwar ta yi kira ga daukacin mambobin kungiyar da su ci gaba da jajircewa wajen aiki sannan su bai wa shugabaninsu hadin kai da goyon baya domin samar da yanayin da ya dace.
A cewar jami’in yada labarai na zauren majalisar, Umar Ma’aji, tuni majalisar da ma’aikatanta suka koma bakin aiki a ranar Talata an ci gaba da gudanar da ayyukan majalisa kamar yadda aka saba.