Kungiyar MAFITA ta horar da matasa dubu 17 sana’o’i

Kungiyar MAFITA ta horar da matasa marasa galihu kimanin dubu 17 sana’o’i daban-daban da suka hada da aikin jakunkuna da takalma da gyaran wayar salula da aikin kafinta da dinki da sauransu. Jami’in Kungiyar Malam Umar Nuhu Muhammad ne ya bayyana haka lokacin da yake zantawa da manema labarai a kan ayyukan kungiyar a Kano. […]

Kungiyar MAFITA ta horar da matasa dubu 17 sana’o’i

Wadansu daga cikin waxanda Kungiyar MAFITA ta horar wajen yaye su

Kungiyar MAFITA ta horar da matasa marasa galihu kimanin dubu 17 sana’o’i daban-daban da suka hada da aikin jakunkuna da takalma da gyaran wayar salula da aikin kafinta da dinki da sauransu.

Jami’in Kungiyar Malam Umar Nuhu Muhammad ne ya bayyana haka lokacin da yake zantawa da manema labarai a kan ayyukan kungiyar a Kano.

Malam Umar ya bayyana cewa tun daga lokacin da aka kafa  kungiyar ta MAFITA shekara hudu da suka wuce take gudanar da ayyukanta a jihohin Kano da Kaduna da Katsina da Jigawa don inganta rayuwar matasan da ba su da galihu da suka hada da almajirai da marayu da nakasassu da ’yan matan makarantun Islamiyya da sauransu.

Kididdiga ta nuna cewa, kaso mafi yawa daga wadanda suka amfana daga kungiyar mata ne wadanda shekarunsu suka kama daga 15 zuwa 24.

A cewar jami’n duk da cewa kungiyar ba ta bayar da jari ga matasan da ta koya musu sana’o’in amma tana yi wa matasan hanyar samun bashin kayan aiki daga bankuna.

“Idan muka yaye matasan mukan kai su bankuna musamman kananan bankunan kasuwanci inda muke yi musu kungiya don su samu bashin kayan aikin sana’ar da suka koya tare da biyan bashin a hankali ba kuma tare da biyan kudin ruwa ba”, inji shi.

Malam Umar ya kara da cewa, ‘“Mukan yi kokarin samar wa matasanmu kasuwa yadda za su shigar da kayayyakin da suke sarrafawa tare da samun abokan ciniki. Akwai kuma nau’o’in matasa da muke horarwa kan aikin kimiyya tare da sama musu takardar shaida daga Hukumar NBTE don inganta ayyukansu.”

Wata daga cikin wadanda Kungiyar MAFITA ta fitar da rayuwarsu daga cikin kunci mai suna Sa’adatu Gambo ta bayyana cewa, a yanzu da ta samu horo a kan dinkin jakunkuna, kuma ta samu madogara wacce take samun abin masarufi don tallafa wa kanta da iyayenta.