Kungiyar Maharba za ta taimaka wajen yaki da masu sace mutane a Taraba
Kungiyar Maharba a Jihar Taraba ta ce a shirye take ta taimaka wa jami’an tsaro wajen yaki da masu sace mutane da sauran masu aikata miyagun laifuka . Shugaban Kungiyar na karamar hukumar Ardo-Kola,Mallam Suleiman Sunkani ya furta haka a a lokacin da yake zantawa da wakilin Aminiya. Yace yan Kungiyar ta Maharba ta kasance […]
Kungiyar Maharba a Jihar Taraba ta ce a shirye take ta taimaka wa jami’an tsaro wajen yaki da masu sace mutane da sauran masu aikata miyagun laifuka .
Shugaban Kungiyar na karamar hukumar Ardo-Kola,Mallam Suleiman Sunkani ya furta haka a a lokacin da yake zantawa da wakilin Aminiya.
Yace yan Kungiyar ta Maharba ta kasance tana da rajista tare da kai’doji wanda dole kowanne dan Kungiya ya bi.
Mallam Suleiman ya kara da cewa ayyukan yan Kungiyar a daji suke gudanarwa watau harbin namun daji wanda haka din yasa suka fi kowa sanin sirrin daji.
Shugaban Kungiyar maharban ya bayyana cewa kasancewar masu satan mutane da sauran ayyukan laifi a daji suke boyewa maharba in sun sami yardar jami’an tsaro zasu taimaka wajen tarwatsa masu aikata miyagun ayyuka dake boye a dazuka suna cutar da Jama’a.
Ya ce ba dajin da maharba suke tsoron shiga a kasar nan saboda haka bukatarsu ita ce gwamnati ta jawosu a jika a saka su cikin harkar tsaro kamar yadda ya kamata.
Mallam Suleiman ya kara da cewa Kungiyar tana da rassa a dukkan kananan hukumomin jihar wadanda a yanzu ke fuskantar matsalar satar mutane
Ya ce ’yan kungiyar a shirye suke su tallafawa jami’an tsaro don ganin an shawo kan matsalar aikata laifuka a Jihar musamman satan mutane wanda ta hana jama’a walwala.
Shugaban Kungiyar na maharba ya bayyana cewa yan Kungiyar sun bayar da taimakon sun wajen yaki da yan Kungiyar Boko_Haram a shekarun baya saboda jihohin da suka fuskanci matsalar Boko_Haram sun san irin taimakon da ’yan kungiyar maharba suka bayar a yaki da ’yan Boko_Haram.
Yace saboda haka a yanzu ma a shirye suke su bayar da gudunmawarsu wajen fuskantar matsalar tsaro a Jihar ta Taraba
Malam Suleiman ya ce abin da suke bukata shine gwamnati ta rika baiwa yan Kungiyar kudin alawus da daukan nauyin yin masu jinya in sun sami raunuka a lokacin da suke fuskantar masu aikata laifuka.
Ya kara da cewa akwai bukatar a taimaka masu da ababan hawa domin shiga daji a lokutan da bukatar hakan ta taso.