Kungiyar Mahauta ta Jihar Filato ta yunkuro don hada kan ‘ya’yanta
Shugaban Kungiyar Mahauta ta Jihar Filato, Alhaji Abdullahi Abubakar, ya ce kungiyar ta yunkuro don ganin ta hada kan dukkan mahautan jihar. Shugaban ya bayyana wa Aminiya cewa babban abin da suka sanya a gaba shi ne hada kan mahautan jihar don ganin sun zauna lafiya. “Domin ba za a samu ci gaba ba, sai […]
Shugaban Kungiyar Mahauta ta Jihar Filato, Alhaji Abdullahi Abubakar, ya ce kungiyar ta yunkuro don ganin ta hada kan dukkan mahautan jihar. Shugaban ya bayyana wa Aminiya cewa babban abin da suka sanya a gaba shi ne hada kan mahautan jihar don ganin sun zauna lafiya. “Domin ba za a samu ci gaba ba, sai da zaman lafiya. Don haka muke son mahautan jihar nan su hada kansu don a samu damar bunkasa sana’ar fawa a jihar,” inji shi.
Alhaji Abdullahi Abubakar ya ce suna kokarin sake farfado da kungiyar ganin a baya ba a jin duriyarta. Kuma suna samun goyon baya da hadin kai kan haka daga dukkan mahautan jihar da kuma gwamnatin jihar.
Ya yi kira ga gwamnatin Filato ta gyara musu wuraren da suke yanka dabbobi a jihar, domin su zama a tsabtace. Ya kirayi mahautan su rike gaskiya, su guji son zuciya domin idan suka yi haka za su zauna lafiya.