kungiyar mahauta ta karamar Hukumar Toro ta samu sababbin shugabanni

kungiyar mahauta ta karamar Hukumar Toro da ke Jihar Bauchi ta gudanar da bikin kaddamar da sababbin shugabanninta  a garin Magama Gumau kwanan baya.Da yake jawabi a wajen bikin, dan majalisar dokoki ta Jihar Bauchi, mai wakiltar mazabar Toro da Jama’a, Alhaji Tukur  Ibrahim ya bayyana cewa kungiyar mahauta  tana da matukar mahimmanci a tsakanin […]

kungiyar mahauta ta karamar Hukumar Toro ta samu sababbin shugabanni
kungiyar mahauta ta karamar Hukumar Toro ta samu sababbin shugabanni

kungiyar mahauta ta karamar Hukumar Toro da ke Jihar Bauchi ta gudanar da bikin kaddamar da sababbin shugabanninta  a garin Magama Gumau kwanan baya.
Da yake jawabi a wajen bikin, dan majalisar dokoki ta Jihar Bauchi, mai wakiltar mazabar Toro da Jama’a, Alhaji Tukur  Ibrahim ya bayyana cewa kungiyar mahauta  tana da matukar mahimmanci a tsakanin jama’a, lamarin da ya sa yake tare da ita.
Ya ce  idan babu  biyayya shugabanci ba zai tafiyu ba, don haka ya yi kira ga ’yan  kungiyar  su cigaba da yi wa wadannan shugabanni da aka zaba biyayya.
Daga nan ya ba da tabbacin cewa zai  yi kira ga gwamnati kan ta tallafa wa wannan kungiya.
Shi ma a nasa jawabin, shugaban kungiyar mahauta ta Jihar Bauchi, Alhaji Baba Sarkin Fawa ya yi kira ga sababbin shugabannin kan su ji tsoran Allah su yi adalci ga ’yan wannan kungiya da  al’umma gabaki daya.
Har ila yau ya yi kira a gare su kan su wayar wa mahauta kai kan a tabbatar da ana samun dabbobi masu kyau da lafiya don  yankawa. Ya ce, “Ku tsaya wajen ganin dukkan dabbar da ba a yarda da ita ba, kada a yanka ta a sayar wa jama’a naman”.
Daga nan ya yi  kira ga mahautan  karamar hukumar ta Toro kan su cigaba  baiwa wadannan shugabanni goyon baya da hadin kai don a cimma nasara, sannan ya bukaci su mayar da hankali wajen sanya ’ya’yansu a makaranta, kuma su ma kansu iyaye su rika neman ilimi domin sana’a ba ta hana karatu, “Don haka ku yi kokari ku rika sanya ’ya’yanku a makaranta”. Inji shi.
A nasa jawabin sabon shugaban kungiyar, Alhaji Amadu Saleh Tulu ya bayyana matukar farin cikinsa da wannan goyon baya da mahautan suka ba shi, saboda haka ya ba da tabbacin shi da sauran wadanda aka zaba za su yi iyakar kokarinsu wajen rike wannan amana da aka damka masu.
Ya ce, “Za mu kawo cigaba a kan  harkokin wannan kungiya a wannan karamar hukuma”.

Ɗan Aljeriya ya shiga hannu kan safarar makamai a Zamfara

’Yan bindiga sun kashe ’yan banga sun sace mai unguwa a Kaduna

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50

Jami’an Sibil Difens sun kashe mayaƙan Boko Haram 50