Kungiyar Mahauta ta koka kan huldarta da dillalan shanu
Kungiyar mahauta ta Najeriya mai suna National Butchers Union of Nigeria (NBUN) ta koka a kan yanayin huldarsu da wasu dillalan shanu a kasar nan inda suka zargesu da cin zarafinsu ta hanyar amfani da jami’an tsaro. Babban sakataren kungiyar ta kasa Malam Sa’id Ibrahm Adam wanda ya bayyana korafin a yayin wata zantawa da […]
Kungiyar mahauta ta Najeriya mai suna National Butchers Union of Nigeria (NBUN) ta koka a kan yanayin huldarsu da wasu dillalan shanu a kasar nan inda suka zargesu da cin zarafinsu ta hanyar amfani da jami’an tsaro.
Babban sakataren kungiyar ta kasa Malam Sa’id Ibrahm Adam wanda ya bayyana korafin a yayin wata zantawa da Aminiya, ya ce kungiyar ta gudanar da taronta na farkon wannan shekara a birnin Benin ta Jihar Edo inda ta kuma bayyana goyon bayanta a kan shirin Gwamnatin Tarayya na kafa wuraren kiwo da aka fi sani da suna “Cattle Colony” a wasu jihohi a wani mataki na magance rigingimu da ke aukuwa a tsakanin makiyaya da manoma.
Bayanin wanda sakataren ya yi a madadin shugaban kungiyar na kasa Cif John Osamade Adun, ya nuna cewa dillalan shanu na amfani da jami’an tsaro na ’yan sanda wajen kamo membobinsu daga wuraren da suke sana’a zuwa wasu jihohi na daban ana tsare su tare da cin zarafinsu a kan matsalar bashi da ta shiga tsakaninsu, a maimakon binciken lamarin a wuraren da matsalar ta faru.
Da ya juya a kan shirin kafa wuraren na kiwo, babban sakatare na mahauta ya bukaci gwamnati da ta sa al’ummarsu a cikin tsarin ta hanyan kafa mayanka wato abatuwa a wuraren.
kungiyar ta bayyana sana’ar kiwo da ta fawa a matsayin wadanda ke bukatar gudunmuwar juna, inda ta koka a kan asaran rayuka da kasar nan ta fuskanta a baya-bayan nan a sakamakon wasu rigingimu da ake dangantasu da fada a tsakanin makiyaya da manoma, inda ta ce akwai bukatar a goyi bayan gwamnati a kan duk wani shirinta da zai iya kawo karshen fitinar. “Tsarin kafa wuraren kiwon idan ya tabbata zai bunkasa harkoki da dama kamar mayar da kasar nan mai dogaro da kai a fuskar madarar ruwa da na gari, da kirazai don gudanar da aikin jima da fitar da nama zuwa kasashen waje, sai kuma samar da wadataccen takin gargajiya musamman a jihohin da za su amfana daga tsarin,” a cewar kungiyar.