kungiyar Majma’u ta yi bikin mauludi a Abuja(2)
kungiyar Matasa Masu Yaki da Shaye-Shayen Miyagun kwayoyi wato Youth Forum on Drugs Abuse da ke Kano (YAFODA) za ta fadada ayyukanta zuwa wasu jihohin arewacin kasarnan domin ci gaba da aikin ilmantar da matasa illolin shan miyagun kwayoyi.A jawabinsu daban-daban, Shugaban kungiyar Malam Abubakar Mai Tumaki da Sakataren kungiya Malam Abdulrazak Ibrahim da kuma […]
kungiyar Matasa Masu Yaki da Shaye-Shayen Miyagun kwayoyi wato Youth Forum on Drugs Abuse da ke Kano (YAFODA) za ta fadada ayyukanta zuwa wasu jihohin arewacin kasarnan domin ci gaba da aikin ilmantar da matasa illolin shan miyagun kwayoyi.
A jawabinsu daban-daban, Shugaban kungiyar Malam Abubakar Mai Tumaki da Sakataren kungiya Malam Abdulrazak Ibrahim da kuma jami’in hulda da jama’a na kungiyar Malam Isah Bello sun bayyana cewa suna samun kyawawan nasarori wajen fadakar da matasa illolin shaye-shaye wanda hakan ce ma ta sanya suka yanke shawarar fadada ayyukansu zuwa wasu jihohin arewacin kasar nan.
Har ila yau, shugaban ya ce kungiyar tana da alaka mai kyau tsakaninta da hukumomin tsaro da ke Jihar Kano tare da Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun kwayoyi (NDLEA).
A karshe shugabannin kungiyar sun bayyana cewa suna gudanar da gangami na wayar da kan dalibai a makarantu da kuma tashoshin motoci, inda suka ce “muna jan hankalin al’umma muhimmancin barin shan miyagun kwayoyi ta yadda za a kawar da wannan matsala musamman ganin cewa lokaci ya yi da kowa zai zamo nagari cikin al’umma.”