Kungiyar Malamai (NUT) ta ba El-Rufai wa’adin mako biyu
Kungiyar Malamai ta Kasa (NUT), reshen Jihar Kaduna, ta ba Gwamnan Jihar Kaduna wa’adin mako biyu domin ya yi watsi da shirin sallamar malaman Firamarin jihar su kimanin 21,000, wadanda ake ce sun fadi jarabar da jihar ta shirya, ko kuma su shiga yajin aikin sai mama ta gani. Wa’adin, wanda kungiyar ta aike wa […]
Kungiyar Malamai ta Kasa (NUT), reshen Jihar Kaduna, ta ba Gwamnan Jihar Kaduna wa’adin mako biyu domin ya yi watsi da shirin sallamar malaman Firamarin jihar su kimanin 21,000, wadanda ake ce sun fadi jarabar da jihar ta shirya, ko kuma su shiga yajin aikin sai mama ta gani.
Wa’adin, wanda kungiyar ta aike wa gwamnan, zai fara aiki ne daga ranar 6 ga watan Nuwamba zuwa ranar 23 da watan na Nuwamba.
A cewar mataimakin babban sakataren kungiyar, Kwamrade Adamu Ango wanda shi ne ya sanya wa takardar hannu, ya ce idan har wa’adin ya kare, gwamnan bai yi komai ba, to za su shiga yajin aiki kamar yadda suka amince a taron da suka yi da sauran membobinsu.